Hukumar EFCC Na Cigiyar Jamilah Tangaza

0
1189

Rabo Haladu Daga  Kaduna

HUKUMAR yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta\’annati, EFCC ta ce tana neman tsohuwar mai kula da sashin mallakar filaye a Abuja, babban birnin kasa,  Jamilah Tangaza.
Hukumar EFCC ta ce tana neman Jamilah Tangaza ne, bayan wasu rahotanni sun ce jami`an tsaro sun same ta, tana yunkurin ficewa daga kasar ta haramtacciyar hanya don tsallake belin da hukumar ta ba ta.
Wasu jaridun sun rawaito cewa, jami\’an tsaro na farin kaya sun kama wani mutum da fasfo din Jamilah Tangaza, bayan da ya nemi a buga mata hatimi a wani ofishin hukumar shige da ficen kasa da ke garin Chikanda a jihar Kwara.
Jaridun sun ambato wani jami\’in hukumar tsaro ta fararen kaya na cewa Jamilah Tangazar na jira ne ta amshi fasfon nata domin ta tsere daga kasar.
A wata hira da manema labarai , shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya kuma yi karin haske game da halin da ake ciki da tsohon ministan birnin tarayya Abuja, Bala Muhammad, da Ministan tsaro Obanikoro, da kakakin yakin neman zaben tsohon shugaban kasa  Goodluck Jonathan, Femi Fani Kayode da suke a hannu yanzu.
A shekaranjiya Litinin ne hukumar ta EFCC ta kuma kama kakakin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, Dokta Reuben Abati.
\’Yan hamayya da masu sukar lamirin hukumar ta EFCC, na zarginta da kama jami\’an tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ne kawai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here