WASU MUTANE SUN RASA RAYUKANSU A WANI HADARIN MOTA

0
1069

Daga Usman Nasidi

MUTANE biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hadari da ya afku a ranar Lahadin da ta gabata a garin Gada-Biyu da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 4 na yamma lokacin da wata mota kirar Corolla ta afka ma wata babbar motar Tirela.
Hadarin ya samu asali ne lokacin da direban Corollan ke sheka gudu a lokacin ana ruwa, daga nan ne motar ta kufce masa inda ya afka ma Tirelan da ke ajiye a gefen hanya.
Wata majiya ta shaida mana cewa direban motar tare da abokin zaman shi ne suka mutu a hadarin, ya kara da cewa da kyar wasu mutanen garin suka iya curo su daga cikin motar, inda suka wuce da su asibitin Kwali, sai dai awanni kadan da kai su asibitin suke ca ga garinku.
Su ma wasu daga cikin \’yan bada agajin sun rasa rayukansu yayin da birkin wata motar dakon mai ta tsinke, inda nan ma ta yi kansu, take yanke mutane biyu suka rasu, inda da dama suka jikkata.
Amma an garzaya da wadanda suka samu raunukan zuwa asibti domin duba lafiyarsu.
Da aka tuntubi shugaban hukumar kare haddura ta kasa wato FRSC na yankin Yangoji Amadi CO, ya tabbatar da faruwar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here