Daga Zubair A Sada
SHUGABANCIN Najeriya, al’amari ne da ya shafi kaddara daga Ubangijin kowa da komai da ya karbi addu’o’in bayinSa ya samar masu da mafita daga cikin kangin da aka jefa kasar da al’ummominta ciki, Janar mai ritaya, Muhammadu Buhari ya hau karagar mulkin kasar ta Najeriya. Wannan al’amari na Allah ne jama’a da dama suke mantawa suka kasa jira su tsimayi yadda Zai yi da bayinSa.
Wannan jawabin ya fito ne daga bakin Alhaji Babangida Abdu Jayawa Malumfashi a lokacin da yake zantawa da wakilin Gaskiya Ta Fi Kwabo kan ire-iren maganganun da mutane ka yi dangane da mulkin na Muhammadu Buhari.
Jayawa ya ce, ko shakka babu imani cikakke ya kamata kowa ya yi da Allah a kan Shi ne mai shiryarwa ga madaidaiciyar hanya, kuma Zai fitar da kasar nan cikin kangin da ta shiga, muddin aka tuba gare shi aka daina aikata laifuka manya-manya.
Sai ya yi korafi a kan batun da Reuben Abbati ya yi cewa, matsugunnin gwamnatin Najeriya akwai tsafe-tsafe a cikinsa, ana kashe rayuka ana tsafi a gefen gidan da wasu lunguna. Ya ce, to, ai gwamnatin da ya yi aiki a cikinta yake tona wa asiri, domin kuwa mun yi imani Buhari mutumin kwarai ne, kuma Allah ba zai bari matsafa su sami galaba a kansa ba.