WATA RIJIYAR BURTSATSE TA RUFTA DA MUTANE 3 DA SUKA RASA RANSU

0
1065

Daga Usman Nasidi

AN samu wani tashin hankali a titin Hanik Onitsha ,jihar Anambra yayin da mutane 3 suka burma rijiyar burtsatse.
Wani ganau ya bayyana cewa, rijiyar burtsatsen gargajiyar ta samu matsala ne sai wata mata ta gayyaci mutane su zo su yi mata gyara.
“Sun yi ihun neman taimako sai wani dan Kalaba ya shiga domin ceto dan uwanshi,ashe shi ma ajalinshi kenan.
Daga baya kuma wani Bahaushe mazaunin
unguwar ya ce zai shiga amma za a biya shi N100,000 amma shi ma ya makale ciki.”
Wani mutum mai rabo wanda ya shiga ciki amma ya fito da kyar fuskarsa duka a kumbure ya ce aljanu sun mare shi.”
Wani dan sanda mai suna mista Apev ya ce an ciro gawawwakin su 3 kuma a sanar da hukuma akan abin da ya faru.
Shi kuma mataimakin kwamishanan \’yan sandan, Yahaya Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin amma ana gudanar da bincike kan al’amarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here