Ana Lalata Da \’Yan Gudun Hijirar Najeriya

0
983

Rabo Haladu Daga  Kaduna

KUNGIYAR Human Rights Watch ta zargi jami\’an gwamnatin Nijeriya da yin lalata da \’yan matan da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, ta hanyar yi musu fyade da yaudararsu don yin lalata da su.
A wani rahoto da ta fitar, kungiyar ta kuma zargi gwamnatin  da rashin yin abin da ya kamata wajen kare irin wadannan matan da kuma tabbatar da suna da \’yanci kuma suna samun ababen more rayuwarsu.
Rahoton ya ce haka ma ba a hukunta masu cin zarafinsu yawanci masu kula da sansanoninsu da jami\’an tsaro da kuma \’yan banga ne.
A karshen watan Yulin bana kungiyar ta tattaro bayanan yin lalata da kuma fyade kan mata da \’yan mata 43 da ke zaune a sansanonin gudun hijira bakwai da ke Maiduguri , a Jihar Borno.
Kawo yanzu dai babu wani martani daga hukumomin  kan wadannan zarge-zarge.
Sai dai tun ba yau ba kungiyoyin kare hakkin bil\’adama sun sha zargin jami\’an tsaro  da irin wannan aika-aikar, amma mahukuntan sun sha musantawa.
Rahoton ya ce hudu daga cikin wadannan mata da \’yan matan sun fada wa kungiyar yadda aka ba su kwayoyin gusar da hankali suka sha sannan aka yi musu fyade.
Yayin da wasu 37 daga cikinsu suka fadi yadda aka yi musu romon baka da alkawurra aure na karya da na ba su taimakon kudi ko wasu kayyayaki aka yi lalata da su.
Da yawa daga cikinsu suka ce mazajen da suka yi musu hakan sun watsar da su bayan da suka dauki ciki, kuma su da \’ya\’yan da suka haifa na fuskantar kyama daga sauran mazauna sansanonin.
Yayin da wasu takwas daga cikinsu suka ce da farko mayakan Boko Haram ne suka sace su, suka tilasta musu auren su kafin su kubuce su arce zuwa birnin na Maiduguri ashe ko can ba su tsira ba.
Rahoton ya zargi jami\’an tsaro da \’yan banga da mayakan sa-kai da ke aiki tare da dakarun gwamnati wajen yaki da Boko Haram da cin zarafin nasu.
Matan sun kuma shaida wa kungiyar cewa suna jin tsoron abin da zai biyo ne baya idan suka kai kara a wani wuri cewa ga irin cin zarafin da aka yi musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here