Rabo Haladu Daga Kaduna
SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya umarci a gudanar da binciki kan zargin yin lalata da \’yan gudun hijirar Boko Haram da kungiyar Human Rights Watch (HRW) ta yi.
Wata sanarwa da gwamnati ta fitar, ta ce shugaban ya kadu da jin wannan labari.
Sannan ya ce \”kyautata jin dadin rayuwar wadannan mutane da ke fuskantar barazana abu ne mai muhimmanci ga gwamnatinsa\”.
Sanarwar wacce mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu ya sanya wa hannu, ta ce \’yan Najeriya da ma kasashen duniya su san cewa gwamnati ba za ta dau zargin na kungiyar ta HRW da wasa ba.
Shugaba Buhari ya bai wa babban Sufeton \’yan sandan kasa da gwannonin jihohin da lamarin ya shafa umarnin su gaggauta gudanar da bincike game da batun.
Binciken na su shi zai nuna mataki na gaba da gwamnatin za ta dauka, a cewar sanarwar.
A ranar Litinin ne kungiyar HRW ta zargi wasu jami\’an gwamnatin Nigeria da yin lalata da \’yan matan da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu, ta hanyar yi musu fyade da yaudararsu don yin lalata da su.
Kungiyar ta kuma zargi gwamnatin da rashin yin abin da ya kamata wajen kare irin wadannan matan.
Ta kara da cewa ta samu bayanin yin lalata da kuma fyade kan mata da \’yan mata 43 da ke zaune a sansanonin gudun hijira bakwai da ke Maiduguri, a jihar Borno.
Sama da mutane miliyan biyu ne suka bar gidajensu sakamakon rikicin na kungiyar Boko Haram.