A zaman majalisar zartarwa, wato FEC na wannan makon, gwamnatin shugaba Buhari ta amince da kirkiro sababbin jami’o’i a fadin kasar nan har guda 8.
Gwamnatin shugaba Buhari ta dauki wannan mataki ne a zaman majalisar zartarwa na mako-mako da ta yi a Fadar Gwamnati da ke Birnin Abuja.
A taron da aka yi a Aso Rock , Gwamnatin shugaba Buhari ta yi na’am da karo sababbin jami’o’i guda 8 a fadin Najeriya. Sai dai kaf wadannan jami’o’i ba na Gwamnati ba ne, wato na ‘yan kasuwa ne.
Shugaba Buhari ya jagoranci wannan taro da shi da ministocinsa tare da sauran mukarraban gwamnatin tarayya.
Sababbin Jami’o’in su ne; Jami’ar Anchor a Legas,
Jami’ar Clifford, Jami’ar Coal City, Jami’ar Dominican, Jami’ar Kola Daisi, Jami’ar Legacy da sauransu.
Haka kuma kungiyar kwadago ta kasa wato NLC, za ta zauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da kungiyar kwadago ta kasa NLC, da kuma kungiyar ‘yan kasuwan Najeriya wato TUC domin ganin shugaba Buhari ya kara albashin ma’aikata daga N18000 zuwa akalla N56000 a kowane wata.
|