An Dakatar Da Alkalan Da Ake Zargi Da Cin Hanci

0
902

Rabo Haladu Daga Kdaduna

HUKUMAR da ke sa ido kan al\’amuran shari\’a a Najeriya NJC ta dakatar da wasu manyan alkalai bakwai daga aiki bayan da jami\’an tsaro suka zarge su da karbar cin hanci da rashawa.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da direktan yada labarai na hukumar Soji Oye ya fitar a karshen wani taron da hukumar ta gudanar a Abuja.
Hukumar ta NJC ta ce an dakatar da alkalan ne har sai an kammala yi musu shari\’a kan zargin aikata cin hanci da hukumar tsaro ta farin kaya, wato DSS ke musu.
A watan da ya gabat ne jami\’an DSS suka yi dirar mikiya a gidajen alkalai a sassan kasa daban-daban, inda ta kama su.
Matakin na NJC ya zo ne bayan kiran da Kungiyar lauyoyi ta kasa ta yi na a dakatar da alkalan, tana mai cewa hakan ya zama wajibi matukar hukumar ta na so kimarta ta dawo a idanun \’yan kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here