Ana Shirin Jana\’izar Laftanar Kanar Abu Ali

0
1294

Rabo Haladu Daga  Kaduna

A ranar Litinin ne hukumomin sojin Najeriya ke jana\’izar kwamandan rundunar sojin kasar ta 272 mai kula da tankokin yaki, Laftanar Kanar Muhammad Abu Ali, tare da wasu sojoji hudu.
Kwamandan da sauran sojojin hudu sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke kokarin dakile wani harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai kan barikin sojin kasa na 119 da ke garin Malam Fatori a Jihar Borno.
Haka ma wasu sojojin hudu sun samu raunuka yayin da mayakan Boko Haram 14 suka halaka a cikin artabun na yammacin ranar Asabar.
A shekara ta 2015 ne Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi wa Muhammad Abu-Ali karin girma daga Manjo zuwa Laftanar Kanar tun kafin ya kai shekarun samun karin girman, saboda jaruntar da ya nuna da ta kai ga kwato yankuna da dama daga hannun mayakan na Boko Haram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here