Zamfara: \’An Kashe Mutane 40 A Wata Mahakar Zinari\’

0
949

Rabo Haladu Daga Kaduna

RAHOTANNI daga Jihar Zamfara sun ce kusan mutane arba\’in ne aka kashe a cikin wani hari da wasu \’yan bindiga suka kai kan wata mahakar Zinari.
Haka ma wasu mutane da dama sun bata yayin da wasu suka tsira da munanan raunukka a cikin harin da aka kai ranar Litinin kan mahakar zinarin wadda ke daura da kauyen Bindim na karamar hukumar Maru.
Mazauna yankin sun shaida wa manema  labarai  cewa harin ya zo bayan da \’yan bindigar wadanda ake zaton \’yan fashin shanu ne suka kwashe makonni suna satar mutane don neman kudin fansa.
\’\’Yawancin wadanda suka mutun lebarori ne masu aikin hakar zinari da kuma wadanda suka zo saye.\’\’ In ji wani mazauni yankin, kodayake kawo yanzu hukumomin tsaro a jihar ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here