AN WATSA WA BUDURWA GUBA A KAN NEMAN AURE

0
1132

Daga Usman Nasidi

WATA kyayyawar budurwa na cikin halin tsaka mai wuya a asibitin koyarwa na jami’ar Jihar Legas bayan wasu mutane sun watsa mata ruwan guba a fuska.
Lamarin ya faru ne a kan babban titin Oshodi-Apapa, lokacin da wani mutum ya sauko daga kan babur ya watsa mata ruwan guban a fuska kuma ya tsere.
Rahoton ya ci gaba da fadin cewa, nan da nan aka garzaya da ita asibiti inda aka same ta da kuna a fuska da kirjinta.
Ogochukwu ta bayyana cewa tana zargin wata mata, matar wani saurayinta mai suna Chidi wanda a baya ya nemi aurenta.
“Ina zargin matar Chidi, saboda ta sha yi min barazana tun kafin faruwar wannan lamari. Kuma yayin da aka kwantar da ni, sai ta kira dan uwana tana fada masa wai yanzu aka fara, wannan somin-tabi ne”
Ogochukwu ta ce ba ta amsa neman auren da Chidi ya yi mata ba, amma duk da haka ya nace mata. A yanzu haka tana jinya a asibitin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here