Daga Usman Nasidi
SASHEN injiniyoyin sinadirai na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya sun kafa tarihi yayin da daliban jami’ar suka kera wata matatar mai, wadda take tace mai randa 1 a rana.
Shugaban aiki , Farfesa Ibrahim Ali Muhammad Dabo ya bayyana cewa za’ayi amfani da matatan ne wajen horar da dalibai.
Dabo ya bayyana cewa jami’ar na da ikon gina matatar man fetur wanda ya fi na matatar man Kaduna girma idan gwamnati za ta taimaka.
Ya ce: “ Da farko mun yi niyyar kera matatar mai da ke tace randa 1,000 a rana,amma bisa ga rashin kudi,shi ya sa muka yi mai tace randa daya.
Abubuwan gudanar da shi ne kawai aka sayo daga Hong Kong. Babu wani dan kasar wajen ya sa mana hannu. Dukkan wadanda suka yi \’yan Najeriya ne. “Wannan shi ne aikin sashen mu da kuma horon mu.” Inji shi
Game da cewar Dabo, an kashe kimanin N20million wajen gina wannan matata kuma kashi 80 na kayayyakin da aka yi amfani da su na gida ne. Ya kara da cewa sun yi niyyar yin wannan abu shekaru 15 da ya gabata,amma sai shekarar 2011 aka fara.