Daga Usman Nasidi
SHAHARARREN malamin addinin Islama da ke zaune a Kaduna Sheikh Ahmad Sunusi Muhammad Sunusi Gumbi ya rasu.
Wata majiya daga iyalan shehin Malamin ta bayyana cewar malamin ya rasu ne a wani asibiti dake garin Abuja da misalin karfe 10 na daren jiya Alhamis 10 ga watan Nuwamba bayan yayi fama da rashin lafiya.
Sheikh Gumbi ya rasu ya bar mata biyu da yaya da dama, da jikoki masu yawa.
An yi jana’izarsa yau bayan sallar Juma’a a masallacin Sultan Bello dake Unguwar Sarki.