An Yi Jana\’izar Tsohon Sarkin Musulmi Dasuki

0
920

Rabo Haladu Daga  Kaduna

DUBBAN mutane ne suka halarci jana\’izar tsohon Mai alfarma Sarkin Musulmi na 18 a daular Usmaniyya  Alhaji Ibrahim Dasuki.
Marigayin ya rasu ne ranar Litinin da daddare a wani asibiti da ke birnin Abuja yana mai shekara 93.
Kuma an binne shi ne a birnin Sakkwato, karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Sa\’ad Abubakar na III.
An yi jana\’izar ne bayan idar da sallar Azahar.
Alhaji Ibrahim Dasuki, wanda shi ne mahaifin tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan al\’amuran tsaro, Kanar Sambo Dasuki, ya rasu ya bar \’ya\’ya da jikoki masu yawa
Marigayi Ibrahim Dasuki ya zama Sarkin Musulmi ne a watan Disambar shekara ta 1988 bayan rasuwar Sarkin Musulmi na 17 Alhaji Abubakar Sadik na 3.
Ya kwashe shekara takwas kan karaga kafin gwamnatin soji ta marigayi Janar Sani Abacha ta sauke shi a shekara ta 1996.
An zarge shi da kin bin umarnin gwamnati da kuma yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ba tare da izini ba.
Bayan sako shi daga inda aka tsare shi tsawon shekaru, ya tare a gidansa da ke birnin Kaduna inda ya ci gaba da tafiyar da harkokin rayuwarsa har zuwa lokacin da ya kamu da cutar ajali.
Bayyana sunansa a zaman magajin Sarki Abubakar na III a maimakon dan marigayin Alhaji Muhammadu Maccido Abubakar III ya jawo wata zanga-zanga ta tsawon kwanaki biyar a birnin na Sakkwato wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla goma.
Masu adawa da nadinsa a lokacin na ganin Muhammad Maccido mai ra\’ayin mazan jiya a zaman wanda ya fi cancanta da wannan karaga, maimakon shi Alhaji Ibrahim Dasuki mai ra\’ayin tafiya da zamani.
Marigayin ya nuna rashin jin dadinsa karara, lokacin da jami\’an tsaro suka kai sumame gidansa na Sokoto a lokacin da suke binciken dansa Sambo Dasuki.
Shi dai Sambo, wanda tsohon mai bai wa Shugaba Goodluck Jonathan shawara ne kan harkokin tsaro, yana fuskantar shari\’a kan zargin cin hanci da rashawa.
Batun da ya musanta yana mai cewa siyasa ce kawai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here