Atiku Yana Yi Wa Gwamnatin Buhari Kafar-Ungulu —El-Rufa\’i

0
894

Rabo Haladu  Daga  Kaduna

GWAMNAN Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi zargin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar yana yin zagon-kasa ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
A wata wasika da ya sanya wa hannu, inda yake yin raddi ga zargin da Atiku ya yi masa na saba wa ka\’idojin aikin gwamnati a lokacin da yake rike da mukamai a gwamnatin Olusegun Obasanjo, Nasir El-Rufai ya kara da cewa cin hanci da rashawa sun dabaibaye Atiku ya sa yake tsoron zuwa Amurka.
Nasir El-Rufai ya ce, \”Alhaji Atiku yana son yin takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2019 shi ya sa yake tunanin idan ya bata mana suna zai kai gaci. Jarabar da yake da ita ta son yin mulki ce ta sanya ya goyi bayan \’yan majalisar dokokin da suka yi wa jam\’iyyarmu bore, wanda kuma hakan ke ci gaba domin kawai nuna rashin da\’a ga shugaban kasa.\”
Gwamnan na Jihar Kaduna ya kara da cewa ya goyi bayan shugaba Buhari a zaben da ya wuce kuma zai ci gaba da goyon bayansa domin fitar da Najeriya daga kangin da ta fada a ciki.
A cewarsa, ya kamata Atiku Abubakar ya yi wa duniya bayani kan rahoton binciken da wani kwamitin majalisar dokokin Amurka ya yi kan yadda aka shigar da fiye da $40m na kamfanin Siemens cikin kasar, kuma aka sanya su a asusunsa da na daya daga cikin matansa.
El-Rufai ya kara da cewa, \” Sakamakon rahoton ba boyayye ba ne domin kuwa yana nan a shafukan intanet\”, yana mai cewa tsoron shan dauri ne ya hana Atiku zuwa Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here