DAGA USMAN NASIDI
WASU kungiyoyin matasa sun rufe kofar shiga majalisar dokokin kasar, suna cewa ba za su gusa ba sai ‘yan majalisar sun sauya halayensu, sun bi sahu a yakin da gwamnatin kasar ke yi da cin hanci da rashawa.
matasan dai na zargin cewa babu abin da ‘yan Majalisar suka sa a gaba face son zuciya, lamarin da suka ce ba zai haifar wa Najeriya alheri ba.
Matasan, wadanda suka yi gangami a mashigar majalisar dokokin Najeriyar sun ce sun dauki wannan matakin ne don nuna goyon bayansu ga aniyar shugaba Buhari, ta yaki da cin hanci da rashawa, yakin da suka ce wajibi dukkan masu kishin kasar su shiga tafiyar.
A cewarsu sai da suka tsaya suka yi nazarin dabi’un ‘yan Majalisar dokokin Najeriya, kafin su kai ga zanga- zangar tasu ta zaman dirshan, amma sun fahimci cewa, kamar yadda suke zargi ba kishin kasa ba ne a gaban ‘yan majalisar.
Gangamin matasan dai ya samu halartar wasu daga fitattun masu fafutuka, ciki har da sanannen mawakin nan Charley Boy.