Babban Bankin Nijeriya Zai Bai Wa Manoman Rani Sama Da Dubu 10 Rance A Jihar Bauci-Mas\’udu Tulu

    0
    3305

    Isah Ahmed Daga Jos

    MALAM Mas\’ud Ibrahim shi ne Mukaddashin Darakatan  kula da sashin bayar da basussukan  noma da bunkasa kananan masana\’antu na babban bankin Nijeriya da ke Bauci. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu kan abin da ya karfafa wa babban bankin Nijeriya gwiwar fito da shirin na samar da rancen kudade ga manoma,  da  ake kira Anchor Borrower\’s Programme [ABP].  Ya bayyana cewa manoman rani sama da dubu 10 ne zasu
    amfana da wannan shiri a jihar Bauci. Ga yadda tattaunawar ta kasance

    GTK; Mene ne ya karfafa wa  babban  bankin Nijeriya gwiwar  fito da wannan shiri na bayar da basussuka ga manoman Nijeriya?
    Mas\’ud Tulu; Abin da ya sa babban bankin Nijeriya  ya  fito da wannan shiri shi ne ganin cewa dukkan wata  kasa mai tasowa  a duniya ta dogara ne da  aikin noma da harkokin kere-kere. Domin su ne kashin bayan tattalin arzikin kowace kasa a duniya.
    Don haka a karkashin tsare-tsaren babban bankin Nijeriya, aka fito da wannan shiri na samar da rancen kudade ga manoma,  wanda a turance ake kira Anchor Borrower\’s Programme [ABP]. Domin an lura kananan manoman
    kasar nan sune  suke noma abincin da al\’ummar kasar nan suke amfani da shi.
    Don haka aka fito da wannan shiri domin a tallafa masu, a juna tunanin su  zuwa ga noma irin na zamani, maimakon irin noman da suke yi  na gargajiya  wanda babu kwarewa a ciki.  A  horar dasu  kan noma irin na zamani, a kawo masu  abubuwan da suke bukata kamar taki da magungunan feshi da kudaden da za su biya wadanda za su yi masu aikin kwadago a gonakinsu. Kuma a magance masu dukkan wasu matsaloli da suka
    shafi harkokin kasuwancin amfanin gonar da suka noma.
    Domin ada idan an baiwa manomi bashi, idan  ya  yi noma ya kai kasuwa, wata kila ya fadi. Amma a wannan shiri tun kafin manomi ya shuka amfanin gonarsa ya san farashin da zai sayar da kayayyakin amfanin gonar da ya shuka, kuma ya san wanda zai sayarwa.
    Kuma yanzu abin da yake faruwa a duniya farashin man fetur ya fadi kasa. Wannan al\’amari ya shafi yadda gwamnatin Nijeriya take samun kudaden shigarta  kuma ya shafi darajar kudinmu a nan cikin gida Nijeriya.
    Shi ya sa babban bankin Nijeriya ya fito da wannan shiri don  bunkasa dajarar kudadenmu. Domin kudaden da muke kashewa wajen  shigo da kayayyakin abinci suna da matukar yawa. A bara kadai an kashe kudi Naira Tiriliyon 1 da Biliyan 300 wajen shigo da shinkafa da alkama da sukari. Bayan  za mu iya noma wadannan kayayyaki a Nijeriya. Don haka mene ne zai hana mu, noma wadannan kayayyaki domin mu yi tsimin wadannan
    makudan kudade da muke kashewa, wajen shigo da wadannan kayayyaki daga kasashen waje?

    GTK;Me yasa wannan shiri yake daukar dogon lokaci?

    Mas\’udu Tulu; Ka san duk wani tsari da yazo sabo dole sai an yi masa gurguwar fahimta. Wasu jihohi sun yi wannan shiri, mun ga irin kurakuran da suka yi. Bama son mu fada cikin irin wadannan kura-kurai.
    Shi ya sa aka dauki dogon lokaci ana kafa harsashi mai inganci domin kada a maimaita irin kurakuran da aka samu a wasu jihohi da suka fara wannan shiri.
    Don haka muka dauki tsawon lokaci muna wayar da kan manoma kan su gane cewa wannan rance da za a ba su ba kyauta ne za a ba su ba. Haka su ma bankunan da suka shiga wannan shiri su ma su gane cewa wannan abu
    ribarsu ce kuma ribar kasa ce gabaki daya.
    Sannan suma  gwamnatocin jihohi su gane cewa wannan shiri zai taimaka masu. Haka suma kamfanonin da suke sarrafa kayayyakin amfanin gona, su gane cewa wannan shiri zai taimaka masu. Shi ya sa muka dauki dogon
    lokaci muna kokarin wayar da kan al\’umma kan wannan shiri.

    GTK; Kamar yaya wannan shiri yake a Jihar Bauci?

    Mas\’udu Tulu; To, bayan kaddamar da wannan shiri a Jihar Bauci, mun yi tarurruka. Sakamakon wadannan tarurruka da muka yi, mun fitar da tsare-tsaren da za mu aiwatar da wannan shiri. Da farko mun wayar da kan monama kan wannan shiri, mun sa sun kafa kungiyoyi, mun sa sun yi rajistar kungiyoyinsu a bankuna.  Mun  horar da jami\’an gona da za su je su horar da manoman  a dukkan kananan hukumomin jihar nan guda 20. Mun yi taswirar wannan aiki tun daga farko har karshe.

    GTK; Ya zuwa yanzu manoma nawa ne suka yi rajista da wannan shiri a Jihar Bauci?

    Mas\’udu Tulu;  A yanzu muna da manoma  sama da  dubu 10 da suka yi rajista  da wannan shiri a jihar Bauchi.
    Kuma yanzu za mu fara aikin tantance dukkan wadannan  manoma da suka yi rajista da wannan shiri, a dukkan kananan hukumomin jihar nan. A wannan tantancewa  za mu je mu ga  manoma  mu ga gonakin  da suka tanada.

    GTK; Kamar kudade  nawa aka ware wa  manoman Jihar Bauci?

    Mas\’udu Tulu;  A wannan shiri ba  a kayyade yawan kudin da za a bai wa manoman kowace jiha ba. Abin da shirin ya kunsa  shi ne ya danganta ga yawan manoman da suka yi rajista kuma suka cancanta ne kawai a
    kowace jiha. Domin za a tantance dukkan manoman da suka yi rajista.
    Don haka  za a baiwa kowace jiha ne  iyakar yawan manomanta da suka yi rajista kuma suka cancanta.

    GTK; Kamar wadanne irin kayayyaki ne za a bai wa manoma a wannan rance, kuma yaya tsawon biyan wannan rance yake?

    Mas\’udu Tulu;  Wannan rance da za a bai wa manoman Jihar Bauci, tun da noman rani ne wata 6  ne. Kuma  akwai kwamitin kwararru na musamman da aka kafa  ya bi  ya kididdige komai. Kamar yawan takin da manomi zai yi amfani da shi da maganin feshi da kudin casa da kudin yanka da kudin fatun buhuna da kudin injin ban ruwa  a kowace eka daya. An kiyasta za a bai wa kowane manomi Naira Dubu 300  ne a kowace eka daya.
    Ba wai za a dauki kudin ne a dunkule a bai wa manomi ba.
    A cikin wadannan kudade za a bai wa manomi taki da iri da maganin feshi da injin ban ruwa da kudaden leburori da buhuna da dai sauransu, kuma duk wadannan abubuwa manomi zai  same su ne, bayan ya sami sako ta waya. Kuma ba a lokaci daya ne za a same su ba.
    Bayan haka kuma idan manomi ya tashi biyan wannan rance  da amfanin gonar da ya noma da shi zai biya.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here