NNPC Na Ci Gaba Da Binciken Mai A Arewacin Nijeriya

0
1004

Rabo Haladu Daga Kaduna

KAMFANIN mai na NNPC ya sake komawa yankin Chadi don ci gaba da bincike da nufin gano ainihin adadin mai da iskar gas din da ke karkashin kasa a yankin.
A wata hira da manema  labarai da  shugaban kamfanin man yayi  Dr Maikanti Baru, ya ce NNPC zai yi amfani da wasu manyan na`urori wajen yin binciken.
Ya kara da cewa idan har abun da aka samu ya kai wani mizani, to kamfanin zai dukufa wajen hakar man.
Tun a shekarun 1970 ne wasu masana da kuma kamfanin NNPC suka yi hasashen cewa za a iya samun mai a yankin, kuma tun daga wancan lokacin aka yi yunkuri daban-daban don binciken man amma ana dakatarwa saboda wasu dalilai, ciki har da zargin cewa akwai siyasa a cikin lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here