Rabo Haladu Daga Kaduna
GWAMNATIN Najeriya ta ce matsin tattalin arziki ya sa ta shafe wata 10 ba ta biya tsofaffin shugabannin kasa alawus dinsu ba.
Sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal, wanda ya bayyana hakan lokacin da wasu \’yan majalisar dattawa suka kai masa ziyara a Abuja, ya kara da cewa ba a bai wa tsofaffin shugabannin kasar alawus dinsu ba ne saboda babu kudin da za a biya su.
Ya kara da cewa tsofaffin shugabanni irin su Goodluck Jonathan, Olusegun Obasanjo da Shehu Shagari suna bin gwamnati alawus tun watan Janairu.
A cewarsa, \”Akwai sashen da ke kula da biyan alawun sin tsofaffin shugabannin kasar amma a halin da ake ciki babu kudi a sashen.
Muna sane da boren da wasu \’yan Jihar Bayelsa ke yi cewa ba a bai wa tsohon shugaba Jonathan alawus dinsa ba, sai dai mun yi musu bayani cewa ba shi kadai ba ne ke fama da wannan matsala.\”
Najeriya dai ta fada matsanancin rashin kudi sakamakon faduwa farashin mai da kuma zargin da ake yi wa gwamnatocin da suka gabata na sace kudaden.