AN KASHE MUTANE 3 A WANI RIKICI A SULEJA

0
1039

Daga Usman Nasidi

HUKUMAR \’yan sandan Jihar Neja ta tabbatar da mutuwar mutane uku a wata hatsaniya da ta kaure a garin Suleja a ranar Litinin 21 ga watan Nuwamba.
Kakakin hukumar \’yan sanda ASP Bala Elkanah ya bayyana wa manema labarai a ranar  Talata 22 ga watan Nuwamba a garin Minna, sai dai ya ce jami’ansu sun tabbatar da zaman lafiya a garin.
Elkanah ya bayyana abin da ya sabbaba rikicin, inda ya ce “wani barawo da ya sace wayar wani mutum, sai ya caka wa mutumin wuka yayin da yake kokarin binsa da gudu. Nan da nan jama’a suka bi shi suka kama shi, inda su ma suka caka masa wuka.
Daga bisani sai \’yan sanda da ke sintiri suka iso wurin, inda suka garzaya da mutane uku da suka jikkata zuwa asibiti, sai dai da isar su Asibiti suka ce ga garinku.
“Amma yanzu mun dawo da zaman lafiya, don haka muna bukatar jama’a da su ci gaba da gudanar da ayyukansu da yau da kullum ba tare da karya doka ba, mu kuma za mu ci gaba da gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata laifin,” inji Elkanah.
Wani shedar gani da ido ya bayyana ma cewar \’yan sanda sun karkatar da ababen hawa dake kan hanyar shataletalen Sarki da Ofishin \’yan sanda na B. hakan ya sanya matafiya masu zuwa Abuja canza hanyar da za ta fitar da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here