An Kashe \’Yan Sanda 128 Cikin Wata Uku

0
1099

Rabo Haladu Daga Kaduna

BABBAN Sufeton \’yan sandan Najeriya ya ce jami\’ansa 128 ne suka mutu sakamakon hare-haren da masu tsattsauran ra\’ayi suka kai musu a bakin-aikinsu.
Wata sanarwa da kakakin rundunar \’yan sandan kasar DCP Don N. Awunah ya aike wa manema labarai ta ce an kashe jami\’an \’yan sandan ne a sassa daban-daban cikin wata uku.
Sanarwar ta ambato Babban Sufeton \’yan sandan Ibrahim K. Idris yana bayyana hakan a matsayin wani abu \”mai matukar tayar da hankali\”.
Ya kara da cewa \”wani abin takacin kuma shi ne yadda ake rusa ofisoshin \’yan sanda da kaddarorin mutane.
Sanarwar ta bayyana cewa a kwanakin baya an kashe \’yan sanda a kauyen Dankamoji na karamar hukumar Maradu da ke jihar Zamfara, da garin Abagana da ke Anambra da kuma Okrika da ke Ribas.
Rundunar \’yan sandan ta sha alwashin yin bakin kokarinta domin kula da iyalan jami\’anta da aka kashe.
Ta yi kira ga \’yan kasa na gari su taimaka wa \’yan sanda idan suka gan su a irin wannan hali
A \’yan kwanakin nan dai ana ci gaba da samun taho-mu-gama tsakanin \’yan sanda da wasu kungiyoyi.
Ko da a farkon watannan sai da \’yan sandan suka yi artabu da `yan kungiyar `yan uwa musulmi a Jihar Kano , lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani dan sanda da kuma mabiya kungiyar da dama.
A lokuta da dama ana zargin \’yan sandan da yin amfani da karfin da ya wuce kima idan sabani ya shiga tsakaninsu da jama\’a.
Hakan ne ma ya sa a kwanakin baya Amurka ta nuna damuwa game da asarar rayukan da ake yi a Najeriya, sakamakon arangama tsakanin `yan kungiyar `yan uwa musulmi da jami`an tsaro.
Sai dai \’yan sandan sun sha cewa suna daukar mataki irin wannan ne domin kare kansu.
Baya ga \’yan sanda, sauran jami\’an tsaro da suka hada da sojoji da na kwastam su ma suna fuskantar irin wadannan matsaloli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here