APC Ta Lashe Zaben Jihar Ondo

    0
    1084

    Rahotannin Rabo Haladu Da Usman Nasidi Da Hauwa Zubairu

    HUKUMAR zabe mai zaman kanta  ta ce ana ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo  da aka gudanar a ranar Asabar.
    Rahotanni sun ce masu kada kuri\’a a wasu rumfunan zaben sun yi korafi na kawo na\’urorin zabe wadanda basa aiki a mazabar su.
    To sai dai mataimakin Daraktan yada labarai na hukumar zaben Mr Nick Dazang ya ce an samu nasara a wannan zabe duk kuwa da wasu korafe korafe da aka samu daga jama\’a.
    Hukumar zaben INEC ta ce za ta tabbatar an sanar da sahihin sakamakon zaben.
    Jam\’iyyu 28 ne dai suka fafata a zaben.
    Kuma zaben na jihar Ondo ya dade yana daukar hankalin al\’umar yankin ganin irin barakar da ta kunno kai tun wajen tsayar da \’yan takara a jam\’iyya APC da ta PDP

    Hukumar zaben ta ayyana dan takarar gwamnan jihar Ondo a karkashin jam\’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben jihar da aka yi ranar Asabar.
    Rotimi Akeredolu ya samu kuri\’a 244, 842, yayin da mutumin da ke biye masa, dan takara a karkashin jam\’iyyar PDP, Eyitayo Jegede ya lashe kuri\’a 150,380.
    Babban baturen zaben jihar Farfesa Ganiyu Ambali, wanda ya bayar da sakamakon zaben, ya kara da cewa mutum 1,647, 976 ne suka kada kuri\’unsu.
    Sai dai jam\’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaben, tana mai zargin hukumar zabe da hada baki da jam\’iyyar APC wajen yin magudi.
    Rotimi Akeredolu zai karbi mulki ne daga hannun Olusegun Mimiko na jam\’iyyar PDP, wanda ya kwashe shekara takwas a kan mulki.
    Zaben na jihar Ondo ya ja hankalin \’yan Najeriya sakamakon kai ruwa ranan da aka rika yi tsakanin jiga-jigan manyan jam\’iyyun biyu da ma masu son tsayawa jam\’iyyun takara gabaninsa.
    Yanzu dai jiha daya ce kadai ta rage a hannun jam\’iyyar da ba APC ba a yankin kudu maso yammacin Najeriya, wato jihar Ekiti.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here