GARKUWAN Sakkwato, kuma tsohon Gwamnan Jihar ta Sakkwato, Alhaji Attahiru Dalhat Bafarawa ya amsa bukatar shahararriyar jaridar nan ta Hausa wato, Gaskiya Ta Fi Kwabo domin tattaunawa da shi domin jin ta bakinsa kan al\’muran da suka shafi kasar nan da al\’ummarta da mu kanmu har da shi kansa.
Da zarar an kammala tattaunawar Editan GTK, zai yada wa dubban makarantar wannan jarida amma ta hanyar Online domin ba a fara \’Hardcopy\’ ba tukunna.