WATA UWA TA HALLAKA JARIRIN TA DA SUNAN WAI SHAIDANI NE

0
1161

Daga Usman Nasidi

WATA kotu ta saurari kara da aka shigar gabanta na wata mata da ta hallaka jaririnta, bayan ta yi ikirarin yaron
Shedan ne.
Uwar jaririn \’yar asalin kasar Senegal ta hallaka jaririn ne bayan ta yi ikirarin cewa,wata murya daga sama ta fada mata yaronta shedani ne.
Rahotanni sun bayyana cewa a shekarar bara ne matar ta dawo da zama kasar Senegal tare da babbar \’yarta da mijinta daga Afirka ta Kudu.
Sai dai ana zargin matar tana fama da ciwon tabin hankali da aka fi sani da suna ‘Capragas delusion” wanda ya sanya ta yi wa jaririn nata yankan rago a watan Yulin da ya gabata. Mahaifin yaron ya tarar da matar da yaron kwance cikin jini a kan katifa.
Mahaifiyar jaririn ta bayyana wa jami’in kula da tababbu Richard Furst cewa, a satin da ta haihu ba ta samun walwala da nishadi, tana cikin damuwa. Ta ce takan ji wasu muryoyi suna fada mata cewa yaronta ba mutum ba ne, shedan ne, abin da ban tsoro, inji ta.
Sai dai a watan Satumbar da ta gabata wata kotu ta karyata cewar tana dauke da ciwon haukar a satin da ta haihu da kuma kwanakin da suka biyo bayan haihuwar tata. Kwanaki biyu kafin ta aikata ta’asar ta fada wa mijinta wai ba ta jin dadi, amma ta ki zuwa ta ga likita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here