Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Shigo Da Motoci Ta Iyakokinta

0
966

Rabo Haladu Daga  Kaduna

GWAMNATIN tarayya ta haramta shigo da motoci  ta kan iyakokinta na kasa.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar hana fasa-kauri ta kasa ta fitar inda ta ce dokar ba za ta fara aiki ba sai ranar daya ga watan Janairu mai zuwa.
Hukumar ta ce haramcin ya shafi shigowa da sababbi da kuma tsofaffin motoci, sai dai bai shafi shigar da motoci zuwa kasar ta ruwa ba.
Wannnan mataki na haramcin shigar da motocin ya zo ne bayan da gwamnatin ta haramta shigar da shinkafa ta bakin iyakokin kasar tun daga watan Afrilun 2016.
Hukumar hana fasa-kaurin ta kuma shawarci masu shigowa da motoci ta kasa da su gaggauta kwashe motocin da suka shigo da su a ruwa amma kuma suke wasu tashoshin jiragen ruwa na wasu kasashe makwabta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here