Tinubu Ya Ce Ba Zai Fita Daga Jam\’iyyar APC Ba

  0
  986

  Rabo Haladu Daga Kaduna

  FITACCEN jigon nan na jam\’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya musanta rade-radin da ake yi cewa zai fice daga jam\’iyyar.
  Tsohon Gwamnan na Jihar Legas ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ya sadaukar da rayuwarsa wajen kafa jam\’iyyar don haka bai ga dalilin ficewa daga cikinta ba.
  Ya yi wadannan kalamai ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa ba ya jituwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma yana shirin hada gwiwa da wasu manyan \’yan jam\’iyyar domin kafa sabuwar jam\’iyya.
  Sai dai a cewar Bola Tinubu, \”Wannan gwamnatin ta APC tana son kyautata wa jama\’a kuma hakan ya fi wata bukata ta mutum daya kacal.\”
  Ya kara da cewa \”Za a yi kuskure idan ana yunkurin kyautata wa \’yan kasa, kuma za a yi tsare-tsare wadanda daga baya za a yi wa kwaskwarima. Ana yin kuskure, kuma ana gyarawa.\”
  Shi kan sa shugaban kasa  Muhammadu Buhari ya musanta cewa akwai takun-saka tsakaninsa da Bola Tinubu, yana mai cewa \”Tinubu gagarabadan dan siyasa ne wanda kowa ya san irin gagarumar gudummawar da yake bayarwa wajen ci gaban jam\’iyya mai mulki.\”
  Masu fashin-baki a kan harkokin siyasa na cewa Bola Tinubu bai ji dadin yadda wasu abubuwa ke faruwa a jam\’iyyar APC ba, ciki har da yadda mutunen da yake goyon baya suka sha kaye a zaben Jihar Kogi da Ondo

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here