\’Yan Shi\’a Za Su Kai Gwamnatin Kaduna Kotu

0
907

Rabo Haladu  Daga Kaduna

KUNGIYAR \’yan uwa musulmi wato \’yan shia sun ce za su kai karar gwamnatin Jihar Kaduna saboda haramta ayyukanta da ta yi.
Kakakin kungiyar, Malam Ibrahim Musa, ya shaida wa manema  labarai  cewa matakin da gwamnatin Jihar  Kaduna ta dauka bai yi musu adalci ba don haka za su je kotu ne domin ta bi musu hakkinsu.
Ya kara da cewa gwamnati ta dauki matakin ne domin bata musu suna a idanun al\’umma.
Gwamnatin Jihar  Kaduna dai ta amince da wasu shawarwari na wani kwamitin bincike da ta kafa bayan tashin hankalin da aka yi tsakanin sojoji da mabiya kungiyar a birnin Zariya a watan Disambar da ya wuce.
Tashin hankalin ya yi sanadin mutuwar daruruwan \’yan kungiyar ta \’yan uwa musulmi, a cewar kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International.
Kazalika an kama shugaban kungiyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa da \’yan kungiyar da dama, kuma har yanzu ana ci gaba da tsare shi duk da izinin da kotu ta bayar na sakinsa.

A wata majiya ta gwamnatin jihar ta sanar wa wakilinmu cewa, gwamnati na sane da ayyukan \’yan shi\’ar ciki har da kasancewar ba su yin da\’a ga gwamnati, sannan suna da Gwamnoninsu a jihohin Najeriya, shi kuwa El-Zakzaky shi ne shugaban kasar nan, to wace gwamnati ce za ta amince da kishiyarta a irin wannan hali?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here