Akalla Mutane 200 Suka Mutu A Rugujewar Majami\’a A Uyo

0
947

Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba
MA\’AIKATAN ceto na can  har yanzu iya rai iya fama  suna ci gaba da  zakulo wadanda ake kyautata zato har yanzu ruftawar  ginin majami\’ar Reigners na  ranar Asabar da ta gabata ya  rutsa da su a Uyo babban birnin Jihar Akwa Ibom. An kiyasta akalla mutane sama da metan ne suka gamu da ajalin su a wannan ruguzawar coci amma kuma sai dai gwamnan jihar Emmanuel Udom wanda ke zama babban bako mai jawabi a ranar a cocin yayin bikin bude cocin a bikin da aka shirya na kaddamar da sabon fadan da zai ja ragamar cocin yake jawabi, ginin aka ruwaito ya ruguje, inda Gwamnan ya tsallake rijiya da baya, ba tare da yin ko kwarzane ba .
Ya zuwa hada wannan labari gwamnatin jihar ta bayar da umarni a cafko mata  dan kwangilar da ya yi aikin ginin cocin, wannan shi ne karo
na biyu a Nijeriya da coci ya ruguza ya jawo asarar  rayukan jama\’a masu dimbin yawa.  Kwanan baya a Legas ma an taba samun irin haka. Lamarin da ake danganta shi da kayan gini marasa inganci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here