Ba Najeriya Ce Kadai Ke Fuskantar Tabarbarewar Tattalin Arziki Ba- Dokta Egaga

0
1038

Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba

“TABARBAREWAR tattalin arziin kasa idan \’yan Najeriya suka yi hakuri komai mai wucewa ne musamman irin yadda shugaban Muhammadu Buhari yake bakin kokarinsa ya ga al\’amuran sun daidaita\’\’. Dokta Patrick Egaga malamin jami\’ar Kalaba ne ya yi tsokacin haka yayin hira da wakilinmu na kudanci a Kalaba

Ya ce matsalar tabarbarewar tattalin arzikin kasa ai ba Najeriya ce farau ba ba kuma kanta zai taba zama karau ba musamman irin yadda wannan gwamnati mai ci ta zo ta iske baitul malin gwamnati wadanda suka sauka sun yi wasoson abin da ke cikinta, don haka akwai bukatar a kara hakuri da juriya game da halin da aka tsincin kai domin “ Najeriya ba ita ce farau ba ba kuma kanta ne karau ba idan aka kwatanta da sauran kasashena duniya da suka fada cikin matsalar tattalin arziki ai duk yadda ake ta kururuwar faduwar darajar takardar kudin Najeriya da kuma halin da tattalin arzikin Najeriya ya shiga, ba Najeriya ce farau ba matsalar mu dai kawai ta rashin hakuri da ana ganin tun da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau komai zai zo cikin sauki amma an manta da barnar shekara 16 da mulkin PDP ya yi an bar baitul malin kasa babu abin da ya taka kara ya karya,”inji shi.

Har wa yau Dokta Egaga ya ci gaba da bayar da misalin wasu kasashena duniya da suka fada cikin matsalar karayar arziki amma suka jure abin yanzu ya zama sai tarihi “ Kasa irin Girka ai ta shiga matsalar tattalin arziki wanda ya fi na Najeriya muni amma saboda hangen nesa da kishin kasa da al\’ummar suke nunawa sun fita a wannan mawuyacin hali mai ya sanya mu a nan Najeriya ba za mu yi hakuri ba mu taya shugabanni da addu\’a ba?”, inji shi.

Da aka tambaye shi kan ko ya lura da irin yadda wasu jama\’a suke korafi da gwamnati , ba ta yi masu wani abu ba alhali su ya kamata su yunkuro su ba kasarsu gudunmawa me zai ce a nan? Dokta Egaga ya ci gaba da cewa “ka san tun daga lokacin da kasar nan ta samu mulkin kai matsalar da aka samu shi ne ta yawan dogaro da gwamnati ,wasu ma suna ganin dogaro da gwamnatin ya yi yawa hakan nema ya sanya wasu suke kasa tabukawa kan su komai su nasu tunani gwamnati ce wuka da nama wajen yi masu komai, hakan kuwa ragon tunani ne komai a jira gwamnati a ce ita ce za ta samar wa \’yan wasa aikin yi, ita ce za ta samar da hasken wutar lantarki alhali ba haka ba ne. Ni a nawa gani da kuma fahimta irin tawa babban kalubale da wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammadu Buhari take fama da shi ba , ba zai wuce na yawan dogaro da kuma dimbin bukatu da kowa yake famar jira sai wannan gwamnati ta biya masa. A nan ina nufin tunda Allah ya kawo wannan dan taliki ya kuma kawo shi da manufa mai kyau yana da kuduri mai kyau ga kasa da al\’umarta musamman irin yadda ya ga yana son ya kyautata rayuwar al\’umma yana da gudunmawa mai tsoka da zai bayar wajen gina kasa, saboda kishinta da yake yi da na al\’ummarta.

Wasu gani suke yi tun da ya hau ai komai zai tafi daidai alhali sun manta da irin yadda ya samu kasar don na ji kamar kwanan baya yana cewa kamar ma ya hakura da mulkin a yadda ya samu halin da kasar take ciki na tabarbarewar al\’amura. A nan ka san dan Adam ba a iya masa duk da irin namijin kokarin da yake yi na gyara da kuma aiki ka san dan Adam bai rabo da hassada irin tasa kuma ni na lura taka tsantsan din da yake yi wajen gudanar da mulkinsa da ma nade-naden da yake yi wasu kyashin hakan suke yi saboda su, sun fi so a ba su inda za su yi watanda ta dukiyar qasa irin wadancan mutane sune suke kawo tarnaki gwamanti dai ba zata iyayin abu da yawa ba a lokaci daya dole sai tabi a hankali daki-daki tukuna amma gajen hakurin wasu da an yi abu daya mai kyau sai ka ji suna korafi a kan an gaza a daya misali abu daya da zan bada misali na nasarar da aka samu ta wannan gwamnati shi ne na yaki da \’yan ta\’adda na boko haram matsala da ta zama ruwan dare a bakunan duniya matsala ce ta gida har da wasu kasashen waje ma amma an manta gwamnatin sanda ta zo ta yi alkawarin kawo karshen ta\’addancin nan da zubar da jini da kuma kashe rayukan bayin Allah da ba su ji ba ba su gani ba kamar yadda suka alkawarta fada da su, ga shi yau an samu nasarar murkushe su da can fa ai suna zaune cikinmu suna tsakanin al\’umma yanzu fa? Ai shiru kake ji yanzu na tabbata za ka iya zuwa Maiduguri komai dare ka kwankwasa wa mutum kofa matsayinka na bako ya ba ka masauki amma da fa ? Hakan zai faru kowa ya ga dan uwansa abin tsoro ne abin gudu ne saboda bai san ko waye yake tare da shi ba duk ma yadda aka yi masu lakabi ta\’addanci kowace kasa ana yi amma mu a nan an samu nasarar murkushe namu saboda gwamnati da aka samu ba mai wasa ce ba kuma mai son wasan ba. Babu wani abu da mutum zai yi a duniyar nan da ba za a kalubalance shi ba na yi imani shugaban kasa Muhammadu Buhari gwamnatinsa na da alkibla tana da manufa mai kyau da \’yan kasarta dubi irin ci gaban da aka samu ko zaman lafiyar da yanzu kasar nan ta samu ai ba karamin ci gaba ba ne .”

Daga nan sai malamin jami\’ar ya bukaci matasa da suka fara korafi na rashin cika masu alkawarin daukar aiki ya ce ga alama ta E-payment nan an fara idan suka kara hakuri wasu da daman gaske ma za a ci gaba da daukar su a cewarsa shugabanci ba ya bukatar gaugawa da garaje tun da ya yi alkawari zai cika komai yana binsa daki-daki ne a tsanake shi ya sa ma duk wasu wanda ya zabo ya ba su mukamai sai da ya karancesu ya tabbata ya sansu ciki da bai za su iya rike amanar da ya ba su shi ba mutumin da kowane labari ko shawara ka kawo masa zai yi hanzarin daukar mataki a kai ba sai ya tantance shi ya sa ai wasu ke ta yin korafi ana tafiyar wahainiya shi kuma na lura yana haka ne domin gudun kada gwamnatinsa ta yi kitso da kwarkwata bacin rai da yadda ya samu baitul malin kasar nan ce ya taba cewa saura kadan ma ya rabu da shugabancin ya kyale kowa amma tabbas na tabbata Allah ne kadai ke yi masa jagora kuma shi ne zai ci gaba da yi masa ya samu nasara ya kyale duk wasu masu gaugawa ya ci gaba da mulkinsa ya toshe kunnuwansa daga duk wasu surutai na jama\’a da suke yi, kasar nan har abada ba za ta wargaje ba duk iya daukar dumin da ta yi kasar nan za ta ci gaba da zama a dunkule, na san kuma cewa matsalarmu dan Najeriya ba a iya masa .

Duba majalisar fadarsa mana ai cike take da hazikan ministoci irin su Audu Ogbe, Lai Mohammed da kuma ministan ilimi Adamu Adamu wanda mutum ne mai hangen nesa kwararre kan ilmi dubi da zuwansa irin nasarori da ci gaba ta fuskar ilmi da ake samu, ministan mutum ne mai son aiki ba son aljihunsa ba. Ya rike mukamai na gwamnati, da dama wadanda ba na gwamnatin ba daban-daban ya san abin da yake yi a aiki .Daga majalisar ministocinsa ka taba ganin akwai wani bara gurbi wanda za a ce yau bai cancanta ba ? Ka taba ji yau cikin ministocinsa da akace cikin shekara xaya da mulki ya mallaki gidaje a qasashen waje? Ko wasu manyan kadarori kafin yanzu ai halayen ministotocin da gwamnatin da ta shude suke yi ke nan na taba samun labarin wani minista a gwamantin da ta gabata ya sayi gida a duniyar wata da yawan wasunsu na da burin gina gidaje a duniyar wata saboda kada ma wani ya rabe su amma tun daga lokacin da wannan gwamnati Allah ya kawo ta sama da shekara daya ka taba jin an yi wa wani daga cikinsu tarzomar zai yi irin wadannan sakarce-sakarcen na zaluntar talakawan Najeriya?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here