Musa Muhammad Kutama daga Lovanta
\’YAN kasuwar shanu da ke Lovanta, Jihar Abiya sun nuna takaicin suna bata masu suna da takwarorin su \’yan kasuwar shanu shanu ta Okigwe, Jihar Imo suka yi da kuma kasuwar su abin ya basu mamamki alhali tsawon shekara goma sha biyu suna kasuwancin su tare a Lovanta, tun daga lokacin da suka kaura daga Umuahiya suka dawo Okigwe ,daga nan kuma suka baro okigwe suka dawo Lovanta sai wani bangare na \’yan kasuwar \’yan Mubi, suka kaurace wa kasuwar suka koma Okigwe cikin watan jiya sai gashi sun ji wasu daga cikin shugabannin waccan kasuwa shanu ta Okigwe na bata masu suna da kuma sunan kasuwar su.
Alhaji Baba Ahmed , sakataren kasuwar shanu ta Lovanta ne ya bayyana haka yayin zantawar da suka yi da wakilinmu na kudanci ya ce kasuwar su tana nan daram tana ci kowace rana ta Allah daga Litinin zuwa Lahadi to amma sai gashi abin mamaki wasu \’yan kasuwa \’yan Mubi da suka ware daga cikin mu suka koma Okigwe tsohuwar kasuwa wadda dalilin rashin tsaro da kuma yawaita yi masu fashi ana kashe masu mutane \’yan kasuwa ya sanya suka kaurato suka dawo Lovanta amma sai ga shi don sun koma can suke bata sunan mu da kuma na kasuwar mu”inji shi.
Ya ci gaba da cewa “a saboda rashin tsaron ne ma a kasuwar shanun ta Okigwe , wata rana 27 ga wata shekara ta 2002 \’yan fashi suka rutsa
Fulani a dakin su suna kirga kudi bayan sun gama cin kasuwa za su yi masu fashi suka yi da dukan kofar dakin su bude ganin cewa mutanen sun ki bude wa barayin kofa ne sai suka zuba wa dakin fetur suka cinna masa wuta suka gudu take mutane goma 12 da ke cikin gidan da barayin suka zo fashi suka kone sannan kuma a wani fashi na daban barayin dai suka sake kashe mutanen mu 8 to amma ka ji don kin gaskiya da son zuciya irin na dan Adam suka ce kasuwar mu ce babu tsaro ai mun zagaya da kai kasuwar ka gani ka ga yadda take ga shanu nan masu yawa sun haura guda dubu ana sayarwa yanzu ace inda ba tsaro a kawo dukiya ta dimbin nairori ace za a ajiye?.Wannan zargi da suka yi ba gaskiya ba ne ai akwai jami\’an tsaro kafin ka shiga da kuma in za ka fita Lovanta”.
Sakataren kasuwar shanu Lovanta ya kara da cewa dalilai uku zuwa hudu ne ma ya sanya suka kaurato daga Umuahiya,Jihar Abiya suka dawo Okigwe Jihar Imo a watan Afrilu na 1994 “dalilin barin mu umuahiya zamanin mulkin soja ne lokacin gwamnan jihar Ike Nwosu lokacin marigayi Sani Abacha na shugaban kasa gari ne yazo ya matsewa kasuwar kasan babu yadda za,ayi kasuwar dabbobi na cikin gari ganin haka ne fa sai gwamnan na wancan lokaci ya gina mana wata kasuwar a Ubakala ,kuma kasuwar tayi mana daji sosai shine mutanen mu sukace basu so shi kuma ya yi amfani da karfin mulkinsa ya ce sai a koma Ubakala, mutanen mu suka fusata shi ne suka ki aka dawo okigwe, lokacin gwamnan jihar Imo na soja Tanko Zubairu ne sannan shugabar karamar hukumar Okigwe Rose Amunike ,ce shugabar karamar hukumar Okigwe aka bamu wuri muka zauna muke kasuwancin mu “.inji sakatare.
Karshe Alhaji Baba Ahmed sakataren kasuwar shanu ta lovanta ya nemi wadancan abokan huldar su da suka bandare da su dawo aci gaba da kasuwanci kamar yadda keyi tsawon shekara goma sha biyu dasu anan Lovanta.Su bar yawo suna bata masu suna da kuma shara masu karya kan abin da ba shi kenan ba.