Ana zargin Saurayi Da Kashe Budurwarsa Kan Kudadenta

0
972

MUSA MUHAMMAD KUTAMA daga  fatakwal

WASU matasa uku  Sotonye Martin,da  Innocent Oluche da kuma  Wachukwu Ugochukwu sun shiga hannun jami\’an tsaro a garin Fatakwal sakamakon zargin su da ake yi da yaudarar wata budurwa ciki har da  saurayinta suka daba mata wuka a ciki  mai suna  Sophia Phillips Horsefall wadda ke aiki a hukumar raya  yankin Neja-Delta wato NDDC. Kamar yadda majiyar tsaro ta sanar, ana zargin  saurayinta Sotonye Martin da aikata haka saboda taki ta yadda tayi  amfani da sunan sa a matsayin magajin ta wanda zai gaje ta yayin da zata bude  asusun ajiya a daya daga cikin bankunan kasuwanci da ke garin Fatakwal.
Bayanai kamar yadda wannan jarida ,  ta samu saurayin sai ya hada baki da abokansa suka gina rami suka binne gawar ta bayan ya kashe ta Da yake yi wa manema labarai karin bayani game da kisan kanwarsa yayan marigayiyar , Amatu Phillips,  ya fadi cewa kanwarsa tana da kudi a susun ajiyar ta na  banki da take da shi, saurayin ya addabe ta da bukatu daban-daban na kudi ita kuma tana kauce masa “ina ga abin da ya harzuka shi kenan  ya kashe ta”.
Phillips ya ci gaba da da cewa  “ Sai ya kirawo ta zuwa gidan abokinsa da suka je can sai ya saya mata lemun kwalba ashe ya sanya kayan sa
maye a ciki yayin da ta sha maye ya ratsa ta sai ya bukaci ta ba shi katin ta na  debi da kanka da kuma lambobin sirrin katin  wato ATM bayan ya karba ta gama fita daga hayyacin ta ne sai ya sanya wuka ya daba mata”. An ci gaba da zargin saurin da yin bakin  kokari na ya ga ta sanya sunan sa a matsayin wanda zai gaje ta, ita kuma ta ki.
Saurayin tare da abokan sa uku yanzu haka  suna  hannun \’yan sanda kuma za a gurfanar da su gaban kuliya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here