Musa Muhammad Kutama Daga Kalaba
\’YAN sanda a Jihar Abiya sun kama wasu mutum biyu da ake zargin su da safarar wani karamin yaro mai suna Obinna Ozuoba,kuma sun yi sa\’ar kubutar da shi daga hannun masu safarar yaran.
Mutanen da ake zargi Rowland Egbe, da kuma wata mace mai suna Chioma Ohajinmmadu, da suka tafi da yaron wajen wanda yake da bukatar ya saya yaron kamar yadda wannan jarida ta samu labari an ce yaudarrasa suka yi da biskit suka tafi da shi kamar za su aike shi wani wuri sai suka arce da shi .
Da yake nuna wa manema labarai masu laifin da ake zargi kwamishinan \’yan sandan Jihar Abiya Leye Oyebade, ya ce, an kamo daya daga cikin su mai suna Rowland Egbe a Obehie ,yankin karamar hukumar Ukwa ta yamma yayin da ita kuma abokiyar huldar tasa Chioma ita kuma aka kamo ta a Ohanku kan hanyar Aba Egbe, inda barawon yaran ya yi ikrarin sayar da yaron kan kudi Naira Dubu 150,kuma an ba shi Naira Dubu 50 kafin alkalami na cinikin.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa yadda suka shirya bayan kama yaron da suka tafi da shi ita Chioma ta yi aniyar daukar yaron matsayin dan ruko ne amma daga bisani sai ta yanke shawarar ta sayar da shi wanda ya sayi yaron zakara ya ba shi sa\’a kuma \’yan sanda sun baza komar su sai sun cafko shi duk ma inda ya shiga ya boye .