Talauci Zai Sanya Ni Sayar Da \’Ya\’yana – Odinaka Ali

0
1159

Musa Muhammad kutama Daga Kalaba

HUKUMAR  da ke hana safara da   fataucin yara wato  NAPTIP, a jihar Ebonyi ta ce ta kama wata mace matashiya mai kimanin shekara   25 da haihuwa, mai suna    Odinaka Ali   bisa zarginta da hukumar take yi na yunkurin sayar da danta mai shekara uku da haihuwa.Mai laifin da na zaune a kauyen Ezilo, karamar hukumar Ishielu ta jihar .

Wasu  mutane ne da suka samu labarin aniyar Odinaka ce suka kyankyasawa yan sanda yayinda ta gama hada baki tsaf da wata wadda za ta nemo mata wanda zai sayi \’ya\’yan  nata ciki har ma da  dan wata takwas  da haihuwa.

Da take yi wa manema labarai  karin bayani jami\’a mai magana da yawun hukumar  Florence Onwa,  ta ce “bayanin da matar tayi masu ,tace ita  ba za ta iya ciyar da \’ya\’yan nata ba ne  shi ya sa ta gwammace ta sayar da su.Ganin cewa ba ta da wani mai taimaka mata shi ya sanya ta yi niyyar sayar da \’ya\’yan kamar yadda ta fada.

Har wa yau kakakin ta NAPTIP ta ci gaba da cewa Odinaka Ali ta ci gaba da gaya masu cewa “mijinta ne ya yi watsi da ita da \’ya\’yan nasu tsawon wata-da watanni  wanda hakan ne ma ya sanya ta gaza ciyar da kanta balle  \’ya\’yan da aka gudu aka bar mata su  sai ta fita ne  ta yi kwadago  ma take iya samun abin da za su ci kuma ga shi tana goyon wani dan nata mai wata takwas da haihuwa .

Matar mai \’ya\’ya uku na cikin tsaka mai wuya saboda babu wani gata ko wanda zai taimaka mata .ta kara da cewa “ni da mijina mutumin garin Amaekpo ne jihar Abiya muna zaune lafiya  wata rana sai muka samu sabani irin na tsakanin mata da miji daga baya kuma muka sasanta bayan haka sai da na shafe makonni ban sa shi a ido ba ganin babu wnai wanda zai ciyar da mu ne ni kuma na shiga fafutukar abin da ni da yara za mu ci ganin komai ya kara  ta\’azzara na yanke shawarar komawa kauye daga bisani kuma na samu wannan yarinyar a wani gidan sayar da abinci tana aiki na fada mata damuwa ta ,daga nan kuma ta ce za ta taimaka min ta samo min wanda zai sayi yaran nawa”.Daga nan muka fara tattauna yadda za a sayar da yaran.inji mai son ta sayar da \’ya\’yan ta uku .

Matar da \’ya\’yan uku duk suna hannun hukumar hana fatauci da safarar yara ta jihar Ebonyi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here