Hukumar Kwastan Ta Dakile Fasa Kwaurin Shinkafar Da Za A Kawota Kano

0
846

Rabo Haladu Daga Kaduna

HUKUMAR hana fasa kwauri ta kasa ta dakile ‘yan kasuwar shinkafa na bayan fage tare da gargadinsu da su kuka da kansu duk randa suka yi arangama za su yaba wa aya zaki.
Wannan bayyani ya fito daga bakin  mai yada labarai na hukumar kwastom ta kasa Mista Atta a Kano bayan gudanar da wani zagaye da hukumar ta umurta da suka hada da Kofar,Unguwa uku,da sauran hanyoyin shigo  da shinkafa Kano ta bayan  fage..
A nasa jawabin Mista Jalo janyo hankalinsu ya yi da cewa su kauce wa karya solar gwamnati a duk inda suka sami kansu domin su zamo ‘yan kasa nagari da gwamnati za ta yi alfahari da shi.
Ya ce sanin kowa ne gwamnatin kasar nan ta hana shigowa da shinkafa ta barauniyar hanya  ba bisa ka’ida ba.
Ya ce idan ‘yan kasuwa suka bada hadin kai to komai zai tafi kamar yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here