Jabiru A Hassan, Daga Kano.
AN bayyana cewa kasafin kudin shekara ta 2017 zai ceto Nijeriya daga halin matsin tattalin arzikin da take fama da shi idan aka dubi irin tanade-tanaden da gwamnatin tarayya ta yi cikinsa.
Wannan tsokaci ya fito ne daga kungiyar tabbatar da shugabanci nagari a karshen taron da ta gudanar na karshen shekara a Kano, inda kuma ta yi fatar cewa majalisar dattawa da ta wakilai za su gaggauta amincewa da wannan kasafin kudi ta yadda gwamnatin Tarayya za ta fara aiki da shi ba tare da samun tsaiko ba.
Shugaban kungiyar Alhaji Bashir Ahmed ya sanar da cewa alamu sun nuna cewa nan gaba kadan kasar nan za ta zamo cikin yanayi mai kyau bisa la\’akari da irin kokarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi wajen dora ta a kan dandamali mai inganci kamar sauran kasashen da suka ci gaba a duniya.
Alhaji Bashir Ahmed ya kuma yi kira ga \’yan Nijeriya da su ci gaba da yi wa wannan gwamnati fatar alheri domin ta cimma kyawawan manufofin ta na bunkasa kasa.