ZUWA GA EDITA Gaskiya tafi kwabo.
INA fatar Edita da ma’aikatansa suna lafiya ,na rubuto wannan wasika ce domin nuna farin cikina da sake farfado da wannan mashahuriyar jarida tamu mai albarka mai tsage gaskiya komai dacinta .Sannan kuma in yi wa masoya da makarantar wannan jarida,musamman masu mu’amala ta kafafen sadarwa na zamani da kuma masu rike babbar waya albishir cewa yanzu za su iya karanta wannan jarida ta intanit ba tare da wata matsala ba.
Kusan kowa ya san wannan jarida wadda jarida ce wacce ke kawo ingantattu da sahihan labaran kasata Najeriya da makwabta har ma da kasashen ketare.
Jarida ce wacce ta yi fice gurin tsage gaskiya komai dacinta ba za mu mance da Editocinta ba tun daga kan na farko wato marigayi Abubakar Imam da kuma har zuwa wanda ya gabata zuwa kuma na yanzu da ke kan kujerar .
Karshe ina kira ga gwamnaonin arewa da su yi dukkan bakin kokari su ga an dawo da wallafa jaridar kamar yadda ake yinta shekarun baya tun da ba kowa ne a wannan zamani yake iya rike babbar waya ba.
Na gode Yarima Ya’u Gangariya
Makarancin jaridar GTK.
Lamba 23 layin Bagobiri
Kalaba jihar Kuros Riba