Za A Shimfida Layin Dogo A birnin Kano

0
1027

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN Jihar Kano ta kare matakin da ta dauka na bayar da kwangilar shimfida layin dogo na zirga-zirga a cikin gari, da za a yi a kan kudi kimanin dala biliyan daya da miliyan dari takwas.
A kwanakin baya ne gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu akan yarjejeniyar shimfida layin dogon da wani kamfani na kasar China, lokacin da ya kai wata ziyara kasar.
Sai dai wasu mutane a jihar sun soki matakin suna masu zargin cewa gwamnatin na shirin karawa jihar bashi ne kawai.
A yayin wata ziyara da ya kai ofishinmu na London, Sakataren Gwamnatin Jihar Kanon, Alhaji Usman Alhaji ya shaida wa manema labarai  cewa aikin gina layin dogon, wani bangare ne na yunkurin gwamnatin jihar na janyo ra\’ayin masu zuba jari.
a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here