Ina Shiga Takara ne Domin Cimma Burin Al\’ummominmu – Sanata Kankwaso

  0
  1188

  MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba

  “NI ina shiga takara ce domin bunkasa al’umma da ci gaban kasa ba domin yin takara” ba wannan kadan daga cikin amsoshin da tsohon Gwamnan Kano kuma sanata mai wakiltar kano ta tsakiya injiniya dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ya  bayyana wa wakilinmu na kudanci  MUSA MUHAMMAD KUTAMA haka   a Kalaba lokacin da ya  halarci addu’o’in fatar alheri da aka yi wa Mininstan Neja- Delta Fasto  Usani Uguru  Usani a Kalaba kuma ya gana ma  da wasu  ‘yan arewa mazauna Kuros Riba ganin cewa ana ta yawai ta  kira ga tsohon Gwamna da ya  fito takarar mukamin shugaban kasa zaben 2019 tun da shi ya zo na biyu zaben fidda gwani  wanda aka yi a 2015. ko ya amsa kiran magoya bayan nasa ?  Ga yadda hirar tasu  ta kasance:-

  GTK: Yallabai barka da zuwa Kalaba Jihar Kuros Riba tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma  Sanata mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa,makarantan Gaskiya Ta Fi Kwabo za su bukaci jin  ko mene ne ya kawo ka Kalaba ?.

  Kwankwaso: Assalamu Alaikum, kamar yadda ka gani mun zo wannan jiha ce ta Kuros riba wannan babban birni nata wato Kalaba domin mu taya dan uwanmu ,abokinmu Minista  na Neja-Delta wato Fasto Usani Uguru Usani murna da kuma yi  masa addu,a  shi ne ya kawo wannan gari kuma Alhamdulillahi ka ga taro ya yi kyau ,an samu nasara an yi taro lafiya an gama lafiya kuma yanzu sai shirye-shiryen mu koma Abuja .Saboda haka mun gode wa Allah kuma mun dauki dama mun gan ku mutanen mu ‘yan arewa wadanda suke zaune a wannan jiha ta Kuros Riba ,mun yi taro da su jiya kuma ga shi kun sake dawowa wasu ma  sun sake zuwa kuma mun roke su da su  zauna lafiya tsakanin su ,kuma su zauna lafiya da jama,ar da suke a wannan jiha , da hukumomi  kuma na hore  su da lallai su tsaya su jajirce dan abin da aka samu a nan a tabbatar an sa yara a makaranta ,kuma idan da iyali da aka bari a can ma a gida a kula da su kuma a kula da yara a can din ma a gida a sanya su a makaranta yadda cikin yardar  Allah gobe ta fi yau kyau.

  GTK: Wasu na  ganin a’a ai taron siyasa ne ka zo mene ne gaskiyar lamarin?

  Kwankwaso: Mmm! Ai yanzu ba lokaci ne na siyasa ba yanzu lokaci ne na tafiyar da aikace-aikacen  gwamnati,Gwamnoninmu da Ciyamominmu da gwamantin tarayya lokaci ne yanzu da za ta tsaya ta yi aiki musamman ma kas an mafiya yawa da gwamantocin da muke da su na kananan hukumomi da na jihohi duk namu ne na APC ,kuma mafi mahimmanci ma ga shi shugaban kasa namu ne na jamiyyarmu ne ta APC, saboda haka yanzu lokaci ne na a ba gwamnati  goyon baya da sauran gwamantoci da hadin kai na su tabbatar mu tabbatar da cewa sun yi aiki wanda ya dace al’umma su ji dadi kuma shekara ta 2019 idan Allah ya kai mu ya kasance gwamnatocinmu sun samu nasara kamar yadda muka samu koma fiye da haka wacce muka samu a shekara ta 2015.

  GTK:Ranka ya dade mene ne  za ka ce ga jama’ar da suke ta kiranka ta kafafen sada zumunta na ka fito ka yi takarar mukamin shugaban kasa a zaben 2019 wace irin amsa za ka ba su?.

  Kwankwaso: To ni dai ban ce kowa ya kira ni in tsaya wata takara ba domin kamar yadda na fada maka lokaci ne na aikace-aikace, mun shiga zabubbuka ba ma gwamnatoci bangaren gudanarwa ba , mu ma wanda muke Sanatoci ,da sauran ‘yan majalisu na  tarayya, da ,yan majalisu na jihohi , da kamsiloli duka lokaci ne yanzu na mu bada kyakkyawan ko karin hadin kai na yadda yake gwamnatoci  za su samu nasara domin nasarar gwamantocin ita ce kadai hanya ta samun nasarar cin zabe na gaba domin mutane Nijeriya , da mutanen duniya ma gabaki daya yanzu kowa so yake yi ya gani a kasa  idan ba,a gani a kasa ba kamar yadda shekarun baya  muka fahimci cewar babu wani abu a kasa muka hadu aka yi canji to gani a kasa ita ce amsa ta farko kuma yanzun aikin mu shi ne duk kan mu mu zo mu hada kanmu a samu nasarori a jihohi , a kananan hukumomi  da ma gwamantin tarayya.

  GTK: Mai girma Sanata an ce ba a fafe gora ranar tafiya ko akwai wani kalami da za ka furta wa masu kiranka din nan da zai kwantar  masu da hankali game da bukatar su a kanka ganin an sanka da kishin kasa da kuma son a gina ta  ?.

  Kwankwaso:  Ni kamar yadda kowa ya sani ba dan siyasa ne da ya shiga siyasa, domin ya yi takara ba na  shiga harkokin siyasa ne domin  tabbatar da cewa al’umma ta samu ci gaba ,jama’a sun samu jin dadi ,an samu tsaro an samu karuwar arziki,a kasa gabaki daya wannan shi ne babban dalilin shigata siyasa.Saboda haka akwai mutanen da suke shiga siyasa domin takara ni ba tsarina ba ke nan  ,ni tsarina  shi ne ni  dan siyasa ne wanda ya shiga wanda duk wani abin da ya samu wanda Allah ne ya kawo,  ya kawo shi sai a karba in dadi ne a karba , in sabaninsa ne ma a gode wa Allah ,kamar yadda ka gani na shiga bangarori daban-daban a harkar siyasar nan na zama mataimakin kakakin majalisa a 1992.ka ga wannan shi ne na fari na zo tsarin mulki ka ga wannan shi ne na biyu , na je na yi Gwamna ka ga wannan tsari na uku ,na zo na yi minista na yi adviser[ mai bayar da shawara) na je neja delta na koma na yi gwamna yanzu ina yin sanata to ka ga ba wai an shiga da cewa ko gwamna za a yi ba ko sanata za a yi duk abin da Allah ya kawo a lokacin da ya  dace to ai a gode masa .

  Mai hankali ba ya shiga siyasa ya ce shi lallai shi sai ya zama kaza duk wani abin da ka ga mutum ya samu Allah ne ya ba shi ,in ya so ya gode masa a wasu lokutan ma na shiga zabe ban yi nasara ba yanzu daga 1992.da na zama deputy speaker [mataimakin shugaban majalisa]zuwa yanzu  a wannan shekaru na shiga zabe sau 15, a cikin 15, na fadi 2. Sannan daya ,kujerar sanata din nan an yi sulhu ka ji uku, kenan  to naci 12 ke nan wannan 2 dana fadi shine 2003 nayi takarar gwamna Allah baisa zan zama gwamnan ba alokacin sai kuma  daya wacce take  ta Legas  shima primary election [zaben fidda gwani] shima wanda Muhammadu Buhari ya zama na daya Rabiu kwankwaso yazo na biyu to kaga idan kaduba a wannan tarihi zakaga da lokacin da ake gwamnati,ta jiha ko ta gwamantin tarayya koma ba,.a komai duk a cikin godiyar Allah ake ana cikin al,umma ana farin ciki ana jin dadi kuma dama tsarin siyasa ke nan  .Amma inason in tabbatar maka da cewar ni tsarina na siyasa tsari ne wanda kullum nake kokarin mu hadu da ,yan uwa da abokan arzuka ,wadanda suke masu son ci gaba a gina wani tsari wanda al,umma zasu ji dadi ,kuma al,umma zasu ce suna jin dadin aikin da ake yi kuma ana samun ci gaba a kasa .

  GTK:Mai girma sanata jamiyyar ku ta APC ita ke jagorancin kasa ,ita kuma ke da  yawan gwamanoni da ,yan majalisu sai gashi ,yan nijeriya na kokawa da matsai da sauran matsala ta tattalin arzikin kasa mai zaku gayawa ‘yan Nijeriya ne domin wasu sun jabaka  sun dana suna jiran 2019 ta zo?

  Kwankwaso:To ! na farko dai shi a kowanne addini mutum yake yi akwai maganar Allah ,tsarin da Allah ya ba kawo shi dole dan Adam sai ya gode masa kuma na tabbata shugabannin mu na kananan hukumomi , na jihohi gwamnatin mu ta kasa wanda gwamantin mu ta kasa ta hada har da  mu da muke senate na tabbata shugaban kasa yana iyaka bakin kokarinsa domin tabbatar da wannan yanayi da ake ciki an canja shi ,arzikin kasa ya dada inganta al,umma sun dada samun ilmi da aikin yi an dada samun harkokinn tsaro sun inganta  da sauran abubuwa mahimmai wadanda dama dan sune ake zaben gwamnati na tabbata musamman wannan sabuwar shekara ta 2017 zamu shiga muna  sa rai abubuwa in Allah ya yarda shugabannin mu zasu tsaya da goyon bayan mu gabaki daya  a dada jajircewa su  canja  abubuwa muna sa rai a ,yan kwanaki kadan a cikin wannan wata kamar yadda tsarin mulki ya tanada watan  12 shugaban kasa zai kawo budget kasafin kudi kuma na tababata majalisar tarayya data dattawa  za mu hadu muyi aiki cikin gaggawa,mu tabbatar cewa wanna budget an fitar dashi yadda ya dace yadda ,yan nijeriya  za su samu sauki ,za su samu ci gaba za su samu jin dadi da kwanciyar hankali a wannan kasa tamu Nijeriya gabaki daya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here