Ya Kashe Uwarsa Saboda Bukatar Jima\’i

0
1634

DAGA Mustapha Imrana

WANI mai sana\’ar Achaba ya kashe uwarsa sakamakon jima\’in da ya bukata.

Mutumin mai suna Segun Ogunkusi ya halaka uwarsa ne a gidasu da ke Ogijova Jihar Ogun.

Dan shekaru 33 Ogunlusi ya ce hakika ya kashe uwar tasa misis Abimbola Ogunlusi mai shekaru 60.

Dan Achabar ya tabbatar wa da manema labarai hakan ne a hidikwatar yan sanda da ke Ogun.

\’Yan Sandan sun kuma gabatarwa da manema labarai wadansu mutanen da suka shahara wajen aikata laifi kamar Fade,Satar mutane,Fashi da makamai da dai sauransu kamar yadda kwamishina Ahmed Iliyasu ya bayyana

Dan Achaba Ogunlusi ya ce sai da ya tabbatar ya kashe uwar tasa ya kuma yayyafa ma gawar Kananzir, amma bayan da taki cin wuta ne sai ya binne gawar domin kowa ya huta.

\”Na caka mata wuka ne a cikinta a lokacin tana kicin saboda daman tana ta ce mini inhar ja yi jima\’i da ita to na kubuta\”.

Ya ce lokacin da abin ya faru su biyu na kawai a cikin gidan.

Ya ci gaba da cewa bayan Gawar taki cin wuta ne sai ya jefa ta a cikin matattara bayan gida da aka fi sani da sokawe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here