Rabo Haladu Daga Kaduna
HUKUMAR yaki da fasa kwauri ta kasa da ke kula da gabar teku a Legas ta kama buhunhunan ganyen wiwi da kudinsu ya kai miliyoyin Naira.
Hukumar ta ce an shigo da ganyen wiwin ne daga kasar Ghana.
Haka kuma a wani samame na daban hukumar ta kama wani takin zamani da kudinsa ya zarta Naira biliyan biyu da bincike ya gano cewa ana iya hada bama-bamai da shi.
Shugaban hukumar mai kula da gabar teku a kudu maso yamamcin Najeriya Umar Yusuf ya ce hukumar za ta ci gaba da sa ido don hana shigowa da duk wasu kayayyakin da aka haramta cikin kasar nan.