Gwamna Ben Ayade Na Kaunar Baki Mazauna Kuros Riba – Barista Musa

    0
    1155

    MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba

    WATO tun daga lokacin da aka girka kujerar mulkin dimokuradiyya a Nijeriya 1999 zuwa yanzu akalla an samu shekara sama da sha uku ana wannan mulki kuma gwamnaoni a kusurwoyi daban daban na kasar na musamman a kudu maso kudu da kudu maso gabas suna nada yan asalin arewacin nijeriya matsayin masu taimaka masu na musamman kamar yadda gwamnan jihar Imo yayi ya nada dan arewa mataimaki  na musamman .

    A jihar Kuros Riba tsawon shekarun nan na mulkin dimokuradiyya ba,a taba nada wani dan arewa ba a wani mukami na siyasa a gwamnatocin da aka yi tun daga kan Donald Duke ,da kuma wanda ya karba hannunsa wato Sanata Liyel Imoke, sai fa a wannan lokaci ne na Sanata Farfesa Ben.Ayade ya nada BARISTA MUSA ABDULLAHI MAIGORO kwararren lauya mataimaki na musamman kan harkokin baki wadanda ba ‘yan asalin jihar Kuros Riba ba wanda a turance ake kira da “S.A. Non Indegenes affairs”.

    A tattaunawar su da wakilinmu na kudanci  ya fadi nasarori da kuma kalubalen da ya fuskanta wajen kan hada al,umma musamman gasu ma banbantan harshe, addini da kuma shiyya .Bakin kabilun  mazauna jihar Kuros Riba sun hada da Ibibio, Ibo da kuma  Hausa-fulani, Yarabawa, da kuma sauran kavilu daba ,yan kuros riba ba.

    Ga yadda hirar su ta kasance.

    GTK: Yi mana bayanin yadda ka ji a nasarra karar da gwamna ya samu da kotun koli ta yanke ta ba shi nasara 9 ga watan Disambar nan?.

    Barista :Alhamdulillahi gaskiya a matsayina na mataimaki na musamman kan harkokin wadanda ba ‘yan asalin jihar Kuro Riba bad a kuma duk wani bako  mazaunin wannna jiha ina matukar farin ciki suma kuma suna nuna matukar farin cikin su  tare da godiya ga Allah s.w.t. wanda ya bada dama aka yi wannan shari’a lafiya ba ka gama lafiya kuma Gwamna Ben .Ayade ya samu nasara wannan ba karamin abin farin ciki ne ba gareni, da kuma duk jama,ar da suke a wannan jiha saboda wannna gagarumar nasara da Ben.Ayade ya samu a shari,a da akayi a kotun koli ranar juma,a 9 ga watan Disamba .

    GTK:Kai ne mataimaki na musamman ga gwamna kan baki wadanda ba ‘yan asalin jiha ba wane irin goyon baya ne zaku ci gaba da bashi kai da al,ummar ka domin yaci gaba da mulkinsa har zuwa wa’adi na zango biyu da kowane dan siyasa yake hankoro?

    Barista : To daman mu a matsayin mu na al,ummar musulmi  baki musulmi da wadanda ba musulmi ba yarabawa ne ,Ibibio ne hausa-fulani  tun lokacin nda maigirma gwamna ya kirkiro da wannan ofishi nawa yana da ni a matsayin mai ba shi shawara ko mataimaki na musamman mukayi alkawari, muka kuma jajirce, cewa zamu goya masa baya kuma zamuci gaba da ba shi goyon baya  na ganin cewa yaci gaba day inn nasara da kuma duk alkawura da ya dauka na siyasa na ci gaban wannan jiha ya aiwatar da su to wannan shi ne alkawarin da mukayi na ci gaban jihad a al’ummar ta musamman yadda ya jajirce cewa  zai ci gaba da yin mulki na adalci wanda zai kawowa alummar jihar Kuros Riba ci gaba , to za mu ci gaba da ba shi goyon  baya  in Allah ya yarda har iya karshen mulkin nasa a wannan jiha.

    GTK:Kawo yanzu shekara daya ken an da aka nadaka mataimaki na musamman kan harkokin baki wadanda bay an asalin Kuros Riba ba yi mana jagora cikin nasarorin da ka samu ?.

    Barista Musa:To hakika Ah! Yau na cika shekara daya  cur da wasu ,yan kwanaki   da aka nada ni mai ba gwamna shawara ,to daga cikin nasarori dana samu farko , n,a hada kan baki mazauna Kuros Riba  in  na ce hausawa ina nufin har da  ‘yan kabilar Ibo, yarabawa da ,yan kabilar Ijaw, da kuma duk sauran baki wadanda ba ,yan asalin kuros riba ba ne ,na biyu na hada kawunan sum un zama tsintsiya madaurin ki daya  sannan kuma matsalolin da ake samu a wasu jihohi na rikce-rikice tsakan in manoma da makiyaya  na yi kokari da iznin Allah madaukakin sarki na yi kokari wadancan matsaloli da ake samu a wasu wurare ba,a samu ba anan Kuros Riba ,don nan hada kan makiyaya  da manoma na wanna jihar na fadakar da su mahimmancin zama lafiya daga ciki babbarv nasara ita ce ta hada kan baki mazauna Kuros Riba mun zama tsintsiya madaurin ki daya .

    Kuma na kawo zam,an lafiya da fahimtar juna tsakanin manoma da makiyaya a wannan jiha.

    GTK:Ba mu sani ba ko ka fuskanci wata matsala wajen hada kan al’umma kamar yadda ka fada mana?

    Barista Musa: To ! kasan bai yiwuwa duk lokacin da mutum ya ce yana so ya hada kan mutane ma babanbanta ra’ayi , mabanbanta addini, to dole za a samu ,yan matsaloli ,dole an samu ‘yan matsaloli wadanda ba za,a rasa ba amma kuma Alhamdulillahi matsaloli ne wadanda ba su taka kara sun karya ba dav taimakon Allah da jajircewa da nayi .

    GTK:Bari a karshe mu ji burin mataimaki na musamman kan baki a kuros riba na ofishinka da kuma al’ummar da kake jagoranta?

    Barista Musa: To ni burina bai wuce duk da ni ne wanda farko Gwamna ya nada a matsayin mai ba shi shawara burina shi ne idan na gama wannan aiki ya zamo an samu ci gaba a wannan jiha musamman baki mazauna jihar Kuros Riba kuma duk wani abin ci gaba da dan asalin Kuros Riba zai  samu na ci gaban dimokuradiyya baki ma sun samu .sanna kuma baki mazauna kuros riba su samu zama  lafiya, su samu habakar tattalin arziki da ci gaba a wannan  jiha   to wannan  shi ne burina.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here