Kuna Ganin Buhari Zai Iya Ladabtar Da Muƙarrabansa?

  0
  7805

  Rabo Haladu Daga  Kaduna

  YAKI da cin hanci da rashawa na cikin batutuwan da shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin aiwatarwa tun lokacin da yake yakin neman zabe.
  \’Yan Najeriya da dama na ganin babu mutumin da ya cancanci ya aiwatar da wannan shiri kamar sa musamman idan aka yi la\’akari da dattakunsa da kuma tarihinsa na kyamar cin hanci.
  A lokacin da yake shan rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015, Shugaba Buhari ya jaddada cewa zai yi yaki da wannan matsala ba tare da sani ko sabo ba.
  Matakan farko da ya dauka na kama jami\’an gwamnatin da ta gabata, wadanda suka hada da tsofaffin manyan sojoji da kuma mai bai wa tsohon shugaban kasar shawara a kan sha\’anin tsaro, Kanar Sambo Dasuki, bisa zargin sace fiye da $2.1bn na kudin sayen makamai domin yaki da kungiyar Boko Haram, sun sa ya samu gagarumin yabo daga wajen \’yan kasar da kasashen waje.
  Sai dai zarge-zargen cin hancin da ke ci gaba da mamaye wasu manyan jami\’an gwamnatinsa da kuma halin ko-in-kula da ake ganin yana nunawa sun sanya alamar tambaya kan shirinsa na yaki da cin hanci da rashawa.
  A wannan shekarar kadai, an zargi jami\’an gwamnatinsa da dama da cin hanci cikinsu har da shugaban rundunar sojin kasa Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, wanda ake zargi da mallakar manyan gidaje na sama da $1.5m a birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.
  Kodayake babban jami\’in rundunar sojin ta Najeriya bai musanta mallakar gidajen ba, amma ya ce nasa ne da na iyalinsa kuma ya sanarwa hukumar da ke kula da da\’ar ma\’aikata hakan a takardun da ya mika mata game da kaddarorin da ya mallaka.
  Sai dai ba dukkan \’yan Najeriya ne suka gamsu da bayaninsa ba kuma hakan ya tilasta wa ministan tsaro Mansur Dan Ali fito wa fili ya \’wanke\’ Buratai daga zargin da ake yi masa.
  Shi kansa Mr Buratai ya shaida wa manema  labarai  cewa \’yan ta\’addan da ke amfani da intanet ne suke son ganin bayansa musamman ganin irin nasarar da yake samu a yaki da kungiyar Boko Haram.
  Da alama zargin da aka yi wa shugaban ma\’aikata a fadar shugaban kasa Malam Abba Kyari ya fi jan hankalin shugaban kasar.
  An zarge shi da karbar toshiyar-bakin N500m daga wajen kamfanin sadarwa na MTN domin ya sa a sassauta tarar da aka ci shi ta fiye da Naira tiriliyan daya bayan an same shi da laifin kin yanke layukan wayoyin miliyoyin mutane saba\’in alkawarin da ya yi na yin hakan.
  Abba Kyari dai bai fito fili ya musanta zargin ba, sai dai Shugaba Buhari ya gargadi masu irin wadannan zarge-zarge da su daina, yana mai cewa duk wanda ba shi da shaidar zargin da yake yi wa jami\’an gwamnatinsa ya kamata ya yi shiru.
  Sai dai za a iya cewa masu wadannan zarge-zarge sun ji hudubar shugaban kasar domin kuwa tuni aka fito da \’shaidun\’ da ke nuna cewa wani babban jami\’in gwamnatin, a wannan karon Sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, ya saba wa ka\’idojin aikinsa.
  Majalisar dattawan kasar na zargin sa da yin amfani da kamfaninsa Rholavision wajen karbar kwangilar cire ciyawa a wani sansanin \’yan gudun hijira da ke jihar Yobe a kan fiye da N272m.
  Majalisar ta ce Mr Lawal ya saba ka\’idar aiki wacce ta bukaci ya sauka daga shugabancin kamfanin a lokacin da aka nada shi a matsayin Sakataren gwamnatin tarayya amma bai yi hakan ba sai cikin wannan shekarar.
  Sakataren gwamnatin dai ya musanta zargin, yana mai bayyana \’yan majalisar a matsayin \”masu shirme wadanda ke son ganin bayana.\”
  Wannan batu dai da kuma zargin da ake yi wa shugaban-riko na hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya, EFCC, Ibrahim Magu na cin hanci da rashawa sun tilasta wa shugaban kasar yin magana.
  Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar a makon jiya ta bukaci ministan shari\’a ya yi bincike kan jami\’an gwamnatin da ake zargi da hannu a cin hanci da rashawa kodayake bai ambaci sunayensu ba.
  Masu sharhi na ganin lokaci ya yi da Shugaba Buhari zai dauki matakin ba sani ba sabo a yakin da yake ikirarin yi da cin hanci idan ba haka ba zai faɗi ba nauyi.
  Wani mai sharhi kan al\’amuran yau da kullum Dr Jibrin Ibrahim ya shaida wa manema  labarai  cewa, \”Dole shugaban kasa ya tashi tsaye ya yaki cin hancin da ake zargi yana gudana a cikin gidansa, wato cikin gwamantinsa idan ba haka ba \’yan Najeriya za su yi tunanin cewa akwai mutanen da ba zai iya hukuntawa ba kuma hakan zai sa ya fadi babu nauyi a idanunsu\”.
  Shi ma Malam Bashir Baba, wani mai sharhi da ke Abuja, ya shaida wa manema labarai  cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta soma sanya shakku a zukatan \’yan kasar game da aniyarta ta yaki da cin hanci da rashawa.
  A cewarsa, \”Yunkurin da ake yi na cire Ibrahim Magu daga shugabancin EFCC wata alama ce da ke nuna cewa akwai mutanen da ke cikin gwamnatin Buhari da ba sa so ya yi nasara a yakin da yake yi da cin hanci da rashawa, kuma idan suka yi galabar kawar da shi babu abin da za mu ce sai yi wa gwamnati addu\’a domin kuwa ba za ta iya wannan yaki ba.\”
  \’Yan Najeriya za su saurara domin ganin sakamakon binciken da shugaban kasar ya sanya a yi wa wasu jami\’ansa sanna su gani ko zai iya hukunta su domin gujewa zargin da \’yan hamayya ke yi cewa su kawai yake kamawa da zummar yaki da cin hanci.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here