\’Yan Gudun Hijira 5,000 Ne Suka Nutse A Ruwa a 2016

0
921

Rabo Haladu Daga Kaduna

Yawan \’yan gudun hijirar da suka nutse a ruwa suka mutu a kokarin haura tekun Baharrum zuwa Turai sun kai 5,000 in ji majalisar dinkin duniya.
Bayanan da majalisar ta fita ta cibiyar \’yan gudun hijirar ya hada da mutane 100 da aka bayar da rahoton mutuwarsu a ranar Alhamis, bayan da kwale-kwalensu na roba ya nutse a Italiya.
Hukumar ta ce wannan adadin da ta bayar shi ne mafi yawa na \’yan gudun hijira suka mutu a shekara daya, inda ta kara da cewar suna rasa rayukansu ne sakamakon rashin kyawun yanayi da jirgi mara inginci da kokarin kaucewa hukuma a lokacin da suke yin bulaguron.
Majalisar ta dinkin duniya ta ce ya kamata nahiyar Turai ta tsara dokar da ya kamata abi wadda za ta samarwa \’yan gudun hijrar kariya domin lafiyarsu.
Kusan \’yan gudun hijira 360,000 suka shiga nahiyar Turai ta cikin ruwa, yawancinsu sun isa Italiya da Girka kamar yadda hukumar kula da \’yan gudun hijita IOM ta ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here