Ya Dora Alhakin Tsawwala Farashin Kaya A Kan \’Yan Kasuwa Marasa Tsoron Allah

0
949

MUSA MUHAMMAD KUTAMA  Daga Kalaba

SHUGABAN kasuwar dabbobi ta Jihar Kuros Riba Alhaji Isyaka Muhammad Hadeja, ya dora alhakin karin farashin kayayyaki da ake fama da shi a kasar nan a kan wasu ‘yan kasuwa marasa tsoron Allah da kuma tunani.Musamman idan aka ce wasu bukuwa da dabi’a ko na al’ada lokacin su ya yi a kasar nan .

Alhaji Muhammad Hadeja ya bayyana haka a hira da wakilinmu na kudanci a Kalaba ya ce “ Karin farashin kayayyaki sharrin ‘yan kasuwa ne ake dora wa gwamnati laifi amma babu ruwan  gwamnati.”

Hanya daya da dan kasuwar yake gani idan gwamnati ta bi ta za ta bille musammamn ma idan ta hada da daukar mataki shi ne na kafa hukumar kayyade farashin kaya kamar yadda aka rika yi a gwamnatocin da suka gabata suka yi wannan ita ce hanya kadai da zai magance tsawwala farashin kaya da ‘yan kasuwa  suke yi a kasar nan “Alhamdulillahi ina rokon gwamnati ta sanya idanu a kan abin da ke gudana na kasuwanci da halayen wasu ,yan kasuwar dole gwamnati sai ta taimakawa talakawa   wajen kafa hukumar kayyade farashi ba kowa ya kawo kaya ya kasa ba abin da ya ce a saya abishi da haka ba indai gwamnati ba ta yi gyara ba to haka kowa zai ci gaba da sanya farashi daidai da son ransu talakawa na fama da matsi ana dora wa gwamnati laifi alhali laifin na ‘yan kasuwar ne”inji Hadeja .

Da yake tsokaci game da farashin dabbobi musamman lokutan kirsimeti da na sabuwar shekara da ke karatowa dan kasuwar ya dora alhakin karin farashin da yadda wasu masu sufurin motoci ke kara wa motocin kudin dakon kaya da kuma kuka da yadda ake takura masu a kan hanya wajen bai-miko da jami’an tsaro da ke yin sintiri kan hanya ke yi masu ne wanda hakan ya tilasta wa ‘yan kasuwar da su yi karin farashi.

Shekarar da ta gabata farashin raguna na kamawa ne daga naira dubu 45 zuwa 50 yayin da a bana kuma farashin ya tashi daga farashin naira dubu 60 zuwa dubu 70, karin kudin mota da ke yi masu dakon kayan daga kasuwannin arewa idan sun sawo dabbobin zuwa  kudu a shekarar data gabata a cewar dan kasuwar ana kawo masu kayan akan farashin naira dubu 300 yayin da a bana kuma  farashin ya haura zuwa naira dubu 500 har naira dubu 600 muna biya “injishi wanda hakan ke sanyawa dole farashin dabbobin ya tashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here