An Fitar Da Jaddawalin Wasan kwallon Primier

    0
    835

    Musa Muhammad Kutama, Daga Kalaba

    A yayin da nan da mako biyu masu zuwawato 14 ga watan da muke ciki   ake sa ran fara gasar wasan kwallon kafa ta premier a Najeriya ,hukiumar shirya gasar wato LMC, ta fitar da samfurin kwallon da za,a yi amfani da ita a gasar ta kasa da za a gwabza tsakanin kungiyoyin wasan kwallon kafa na Najeriya.

    Bayanan da kuma jadawalin gasar da hukumar ta aike wa  jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta imel ta  samu  ya nuna zakarun gasar Enugu Rangers za su fara kare kambunsu ne da takwarar ta  Abiya Warriors sai kuma karawar da za ta fi daukar hankalin masoya kwallon kafa ita ce wadda za a yi tsakanin kungiyar wasan kwallon kafa ta Enyimba ,Aba da kuma Sunshines ta Akure.

    Ga yadda kungiyoyin za su fafata da junansu kamar haka: Enyimba FC da  Sunshine Stars
    Kano Pillars da  FC Ifeanyi Ubah, Enugu Rangers da  Abia Warriors, MFM FC da  Niger Tornadoes, Shooting Stars da  Lobi Stars,abs fc da Akwa United ,Remo stars da Plateau United ,
    Katsina United da Gombe United,Rivers United da Elkanemi Warriors, Wikki Tourists da Nasarawa United.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here