Musa Muhammad Kutama Daga Fatakwal
GWAMNAN jihar Ribas Nyesom Wike, ya ce bayyana dalilan da suka sanya ya halarci daurin auren ‘yar tsohon shugaban majalisar wakilai, kuma Gwamnan jihar Sakkwato a yanzu Aminu Waziri Tambuwal,duk da banbancin akidar siyasa tsakanin su, ya yi haka ne domin ya kara nuna wa ‘yan Najeriya cewa kasa daya ake kuma al’umma daya.Wike ya furta haka ne sa’ilin da ya kai wa mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ziyarar ban girma a fadarsa.
Gwamnan wanda Alhaji Aminu Tambuwal Gwamnan jahar Sakkwato ya jagoranta zuwa fadar mai alfar mar domin gaisuwar ban girman ya ce yana da yakini duk yadda aka kai da cakudawa Najeriya ba za ta wargaje ba, daga nan ya gargadi masu neman wargajewar kasar nan da “su kuka da kansu hakar su ba zata cimma ruwa ba”inji shi.
Karshe Gwamnan na jahar Ribas ya jinjinawa sarkin musulmin bisa kokarinsa na hada kan al’umma ba tare da nuna wani bangaranci ba.
Da yake mayar da jawabi mai alfarma sarkin musulmi ya yaba wa Gwamnan Ribas bisa dagewa da ya yi kan kafafunsa na ganin Najeriya ta ci gaba da zama dunkule ba tare da nuna wani banbanci ko bangaranci ba.Daga nan sai ya bukaci sauran shugabanni da su yi koyin da akida irin ta Gwamnan Ribas na ganin an ci gaba da zama kasa daya.