Musa Muhammad Kutama Daga Kalaba
WANI saurayi mai suna Elvis ya kashe budurwarsa a Legas ya jefa gawarta cikin tanki daga bisani shi kuma ya arce .Rundunar ‘yan sanda jihar Legas wadda ta ba da sanarwa ga manema labarai hakan ta ce, bayan da matashin ya kashe budurwar tasa ya gudu ba a san inda yake ba, a halin yanzu, amma ta sha alwashin duk ma inda ya je sai ta zakulo shi .
Kakakin rundunar Dolapo Badmus, ya ce saurayin da ya kashe budurwar tasa kafin ya aikata laifin yana zaune a layin John Omolaja , yankin Obadore, da ke birnin Legas .