Gwamnatin Jihar Katsina Ta Lashi Takobin Ciyar Da Jihar Gaba :Muhammed Kabir Dankaura

0
740

Rabo Haladu Daga Kaduna

BABBAN akantan jihar Katsina Muhammed Kabir Dankaura, ya jinjina wa Gwamnan Aminu Bello Masari , Saboda irin kokarin da yake na kawo wa jihar ci gaba ta sama wa matasa aiki tare da biyan hakkokin ma \’aikata tare da kula da jin dadin ma\’aikata da al\’ummar Katsina baki daya, da ciyar  da aikin gina kasa gaba.
Muhammed Kabir Dankaura ya bayyana wa manema labarai cewa gwamna Aminu Bello Masari ya lashi takobin kawo karshen rashin aikin yi a duk fadin jihar ,ya ce maganar kula da walwalar ma\’aikata kuwa shi ne a kan gaba..
Ya ci gaba da cewa kowa ya san jihar Katsina ita ce a kan gaba wajen noma a duk fadin kasar nan domin  iya  jihar Katsina kadai za ta iya ciyar da Najeriya da ma wasu kasashe makwabta , haka ya sa Gwamna ya yi tanajin taki, irin shuka, kudadan tallafi ga manoma kuma gwamnatin jihar Katsina a shirye take da ta saye duk amfanin gona da manoma suka noma domin kada su yi asara daga baya ta sayar musu a kan rabin kudin da ta saya a wajensu.
Babban akanta ya ce arewa ta wuce kirarin da \’yan kudancin kasar nan ke yi mata na cewa ci-ma-zaune saboda Allah ya yi wa arewa baiwa da mutane masu basira,da albarkatun kasa, ga kiwo na dabobi,da noma domin arewa ce kadai ke ciyar da kasar nan, haka komai da suke ya kama da shi da kudin audiga da gyada manyan da masu hangen nesa suka hako man fetur da su.
A karshe ya yi kira ga al\’ummar jihar Katsina da su ci gaba da yi wa wannan gwamnati addu\’a da fatan alheri, su kuma ci gaba da zama lafiya domin ta haka ne kawai za a sami ci gaba mai amfani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here