Kotu Ta Yanke Wa Dan Tsohon Hakimi Hukuncin Kisa

0
1124

Imrana Abdullahi, Daga Funtuwa

WATA babbar kotun jiha da ke zama a garin Funtuwa ta yankewa dan tsohon hakimin Bakori hukuncin kisa ta hanyar ratayewa.

Mu\’ammar Tukur ya gamu da wannan hukunci ne sakamakon kisan kan da ya yi.

Tukur dan shekaru 32, wanda mahaifinsa  ya taba zama dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Bakori da Danja an yanke masa hukuncin kisa ne saboda yin amfani da wuka ya daba wa wani mai suna Shafir Muktar ya kuma mutu.

A hukuncinsa alkali Abbas Bawale, ya ce masu kara karkashin jagorancin Malam Aminu Garba sun yi kara cewa an yi kisan kai wanda babu wata tantama ko shakka.

Bawale, ya ce an yi shari\’a inda aka tabbatar da shaidun da ya dace a samu guda uku, bayan an gabatar da shaidu biyar tare da shaidun alamomi da kowa zai iya gani da idanunsa.

Abubuwa uku da aka tabbatar sun hada da mutuwar wanda aka kashe, abin da ya haifar da mutuwar da kuma niyyar yin kisan.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 21 ga watan Afrilu 2008 sakamakon fada tsakanin shaidun da aka gabatar da kuma wanda ake tuhuma a wani gidan kallon fim ko nuna majigi.

Alkalin ya kuma tabbatar da cewa dukkan kokarin da lauya Abdul aziz Olagoke ya yi domin kare wanda ake kara bai yi nasara ba.

Inda Lauyan ya ce babu wata shaidar yin amfani da karfe ko kawo shaidar karfen da ake cewa an yi amfani da shi.

Alkalin ya kara da cewa wanda ake kara ya gudu tsakanin shekarar 2008 zuwa 2013 amma sai aka kama shi a makabarta lokacin da ya halarci jana\’izar mahaifiyarsa da ta rasu.

Bawale ya ce wanda aka tuhuma ya bar wurin da lamarin ya faru inda ya dauko karfen da ya yi amfani da shi wajen kisan.

Ya ce an tabbatar da shaidun da ya kamata ba tare da tantama ba kamar yadda doka ta tabbatar don haka an yanke wa mai laifi hukuncin kisa ta hanyar rataye wa.

Alkalin ya kuma bayar da shawarar cewa za a iya daukaka kara cikin kwanaki 90.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here