Ta Kona Kanwarta Da Dutsen Guga

0
942

Musa Muhammad Kutama, Daga Legas

WATA mata mai suna  Mama Emeka da ke zaune a Legas ta fada hannun ‘yan sanda sakamakon kona kanwarta da ta yi da dutsen guga kamar yadda Gakiya Ta Fi Kwabo ta samu labari.Wannan lamari ya faru ne a unguwar Olowora ,layin Fadeyi .

An ce Mama Emeka ta rika kwazzabar kanwar da yawan yi mata fada ba ta jin magana sai ta yi maganinta yarinyar da aka kona da aka sakaya sunan ta majiya ta kusa da Mama Emeka ta shaida wa wannan jarida cewa “tun lokacin da uban yarinyar ya mutu ,uwarta ta yi watsi da ‘yar ita kuma Mama Emeka ta dauke ta tana hannunta take ci mata zarafi tana sanya ta ayyuka kamar baiwa “.Makwabta da suka ga munin cin zarafin ya yi yawa suka sanar wa hukumar kare cin zarafin yara kanana da kuma bautar da su ta ma’aikatar matasa da wasanni  ta jihar Legas su kuma ba su yi kasa a gwiwa ba aka kamata.

Yarinyar wadda duka shekarunta na haihuwa ba su wuce 16. An ce uwar goyonta ta sanya dutsen guga a wuta har sai da ya yi zafi ta fakaici idon yarinyar tana yin wanke-wanke ta dora mata shi a gadon baya ta kona ta.Haka nan kuma an yi zargin Mama Emeka na yi wa yarinyar aski da reza ta shafa mata barkono mai zafi a jikinta

.Rundunar ‘yan sanda shiyyar Ketu sun zo sun yi awon gaba da ita kuma wakilinmu ya tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Legas  Dolapo Badmus game da lamarin ya tabbatar da hakan ya faru matar kuma na hannu ana yi mata bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here